Mata Manoma Sun Yi Fatali Da Tallafin Shinkafa a Jihar Kwara

Mata Manoma Sun Yi Fatali Da Tallafin Shinkafa a Jihar Kwara

  • Ƙananan mata manoma sun yi fatali da tallafin shinkafa da gwamnatin jihar ta raba wa talakawa domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur
  • Matan sun buƙaci gwamnatin jihar da ta samar musu da isassun filayen noma da kayayyakin domin samar da isashshen abinci a jihar
  • Shugabar ƙungiyar ƙananan mata manoma a jihar, Oluwatoyin Abosede Anifowose, ita ce ta bayyana hakan a wajen wani taro

Jihar Kwara - Ƙananan manoma mata a jihar Kwara sun yi fatali da tallafin shinkafa domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Matan a maimakon tallafin, sun buƙaci gwamnatin jihar da ta samar musu da isassun filayen noma da kayan noma domin ƙara bunƙasa samar da abinci a jihar, cewar rahoton The Nation.

Mata manoma sun yi fatali da tallafin shinkafa a Kwara
Matan sun bukaci a ba su isassun filayen noma Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Asali: Facebook

Matan sun bayyana hakan ne a birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara, a wajen taron tattaunawa kan kasafin kuɗin noma na shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu: Gwamnan PDP Ya Manna Hotonsa a Jikin Buhunan Shinkafa, Ya Faɗi Dalili

Manoman sun bayyana cewa ƙananan manoma su ne ke ciyar da ƙasar nan, yayin da manyan manoma ke fitar da amfanin gonansu zuwa ƙasashen waje da rabawa kamfanoni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabar ƙungiyar, Mrs. Oluwatoyin Abosede Anifowose, ita ce ta bayyana hakan a wajen taron tattaunawar kan kasafin kuɗin noma na shekarar 2024 a jihar.

Sun bayyana buƙatunsu

Ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ba ta ba mata manoma muhimmancin da ya dace, inda ta buƙaci gwamnatin da ta samar da shirye-shiryen horaswa da kayan noma domin tabbatar da wadatuwar abinci.

Ta yi nuni da cewa idan gwamnatin jihar ta samar da isassun filayen noma ga mata, hakan zai taimaka musu wajen ƙara yawan kayan amfanin gonan da su ke samarwa.

Hakan a cewarta zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin abinci a jihar.

Gwamnonin jihohi dai sun mayar da hankali wajen rabon kayan tallafi domin rahe raɗaɗin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari Wurin Ibada a Jihar Kaduna, Sun Kashe Malami

Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Rabon Tallafi

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, ƴa ƙaddamar da rabon kayan tallafi a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa za a raba buhunan shinkafa, buhunan takin zamanj domon amfanin gona. Haka kuma gwamnatin za ta ba ɗaliban jihar tallafin kuɗin karatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng