Jihar Edo: Wani Magidanci Ya Halaka Matarsa Kan Sabanin Abinci

Jihar Edo: Wani Magidanci Ya Halaka Matarsa Kan Sabanin Abinci

  • 'Yan sanda sun kama wani magidanci ɗan shekara 21 bisa zargin kashe matarsa kan saɓanin abinci a jihar Edo
  • Kakakin hukumar 'yan sandan jihar ya bayyana cewa tuni aka maida Kes ɗin sashin binciken aikata manyan laifuka
  • Sai dai mutumin ya musanta zargin da ake masa, inda ya bada labarin iya abinda ya san ya shiga tsakaninsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Edo - Hukumar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wani magidanci mai suna Salami Anedu, mai shekaru 21 bisa zargin kashe matarsa ​​biyo bayan saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan abinci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar 'yan sanda ta bayyana magidancin tare da wasu da ta kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.

Yan sanda sun kama mijin da ake zargi da kisan matarsa a Edo.
Jihar Edo: Wani Magidanci Ya Halaka Matarsa Kan Sabanin Abinci Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sanda reshen jihar Edo, SP Chidi Nwanbuzor, ya ce an kama Magidancin ne ranar 30 ga watan Agusta, 2023 ta hannun caji ofis ɗin Fugar.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Wani Matashi Ya Buga Wa Mahaifinsa Taɓarya Har Ya Mutu Kan Ƙaramin Abu

Ya ce a ranar 29 ga watan Agusta, 2023, wani mai suna, Aluaye Momoh, ya kai rahoto wurin 'yan sanda cewa Salami Anedu, ya yi amfani da Itace ya kashe matarsa, Esther Friday.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya faɗa wa 'yan sanda cewa magidancin ya aikata wannan ɗanyen aiki ne a gidansu da ke ƙauyen Ugbekpe a jihar Edo kan ɗan saɓani na iyalai.

Kakakin 'yan sandan ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya rafka wa matarsa wani Icce kuma garin haka ta rasa rayuwarta, Sunnews ta rahoto.

A cewarsa, bayan samun wannan bayanan ne ‘yan sanda suka garzaya inda lamarin ya faru suka cafke wanda ake zargin yayin da aka kai gawar zuwa dakin ajiyar gawa na babban asibitin Fugar.

Mutumin ya bayyana ainihin abinda ya faru

Da yake hira da 'yan jarida, mutumin ya bayyana cewa sun samu saɓani da matarsa ne saboda ta hana shi abinci bayan kammala girki.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari Wurin Ibada a Jihar Kaduna, Sun Kashe Malami

Magidancin ya ce:

"Ta dafa shinkafa ta ce ita zan ci. Ni kuma na je na dafa doya da ƙwai da kaina, ta ce ba zan ci abinda na dafa ba. Ina cikin cin abincin sai ta fara rigima, harda barazanar za ta kira 'yan uwanta su min duka."
"Na ɗauka wasa take, amama sai gata da yayyenta biyu dauke da sanduna, suka jani da faɗa, bayan nan ta tafi gidan Mamata ta kwana. Abun mamaki sai 'yan banga suka zo kama ni wai na kashe matata.
"Bani na kashe ta ba, ban buge ta da Itace ba, 'yan uwanta ne suka zo da Itace amma saboda na yi faɗa da su shi ne suka mun sharrin ni na kashe ta, dama na san bata da lafiya."

Wani Matashi Ya Buga Wa Mahaifinsa Tabarya Har Lahira a Jihar Ribas

A wani rahoton kuma Wani matashi ya yi ajalin mahaifinsa saboda ya hana shi kuɗin da ya nema a jihar Ribas ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi

Ganau ya bayyana cewa da alamu yaron ya sha kwayoyinsu kuma bayan aikata laifin ya yi kokarin guduwa amma mutane duka cafke shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262