Wani Matashi Ya Hallaka Faston Cocinsu Mai Shekaru 60 Da Adda A Jihar Delta
- Jimami yayin da mamban wani coci ya hallaka shugaban cocinsu mai suna Greg Sagie a jihar Delta
- Rahotanni sun tabbatar da cewa matashin ya farmaki Faston ne yayin da ya ke kwance a dakin hutawa tare da 'ya'yansa
- Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Bright Edafe bai ce komai ba dangane da lamarin amma an tabbatar jami'an sun bazama neman matashin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Delta - Wani matashi ya yi ajalin Fasto mai suna Greg Sagie a Sapele da ke jihar Delta.
Matashin wanda mamban cocin Faston ne ya farmaki shugaban cocin nasu da adda a jiya Alhamis 7 ga watan Satumba, Legit.ng ta tattaro.
Yadda matashin ya hallaka Faston a Delta
Vanguard ta tattaro cewa Faston na kwance a dakinsa lokacin da matashin ya shigo inda ya ke.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Matashin ya yi barazana ga 'ya'yan Faston su biyu masu shekaru takwas da 11 yayin da yaran su ka tsere kofar gida tare da ankarar da jama'a.
Wata da ke zaune a yankin ta bayyana yadda abin ya faru yayin su ka kawo dauki wa Faston.
Ta ce:
"Mun rugo da gudu zuwa wurin inda mu ka ga matashin da bai wuce shekaru 20 ba.
"Ya yi mana barazanar cewa idan muka hauro gidan saman zai kashe mu gaba daya inda ya diro daga gidan saman ya tsere."
Meye martani 'yan sanda kan kisan Faston?
Majiyar ta kara da cewa yaran Faston sun gane matashin da cewa mamban cocin mahaifinsu ne.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Bright Edafe bai ce komai game da faruwar lamarin ba, New Telegraph ta tattaro.
Amma wata majiya ta tabbatar da cewa rundunar ta bazama neman wanda ake zargin ruwa a jallo.
Bene ya ruguje tare da kashe mutane a jihar Delta
A wani labarin, wani ginin bene mai hawa uku da ake kan aiki ba'a kammala ba ya ruguje a yankin Okotomi, Okpanam, karamar hukumar Oshimili ta arewa a jihar Delta.
Rahotanni sun tabbatar cewa ginin wanda aka ce sabon Otal ne ake gina wa ya kife da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuli, 2023.
Asali: Legit.ng