NiMet: Za a Zabga Ruwan Marka-Marka a Kano, Kaduna, Sokoto da Wasu Jihohi 20

NiMet: Za a Zabga Ruwan Marka-Marka a Kano, Kaduna, Sokoto da Wasu Jihohi 20

  • Hukumar NiMet ta ce za a tsula ruwan sama a wasu jihohi akalla 20 a yayin da damina ta yi nisa
  • Bincike da masanan da ke hasashen yanayi su ka gudanar ya nuna za a iya samun ambaliya a wurare
  • Duk da wasu su na fuskantar barazana, akwai wasu jihohin da zai yi wahala ayi ruwa mai karfi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - NiMet mai hasashen yanayi a Najeriya ta fitar da sanarwa cewa za a gamu da matsakaici da ruwa mai karfi a wasu jihohin kasar nan.

Premium Times ta ce ruwan saman da za ayi na tsawon kwanaki uku zai shafi jihohi kimanin 25, kuma hakan ya fara tabbata tun daga Alhamis.

Hasashen hukumar tarayyar za a samu karin saukan ruwan sama a wasu jihohin kasar nan 20.

Ruwan sama
Ruwan sama a kasar waje Hoto:businessworld.in
Asali: UGC

Ina ne za ayi ruwan sama kadan?

Kara karanta wannan

Hannatu Musawa da Ministoci 4 da Su ka Jawo Rudani a Cikin Kwana 15 a Ofis

A jihohi kamar Legas, Ogun da Adamawa a Arewa maso gabashin Najeriya, NiMet ta ce za ayi ruwa mara nauyi ne ko matsakaici a makon nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Awanni 24 ake tunanin za a dauka ana tsula ruwan sama a karshen wannan makon, rahoton Daily Trust ya ce ruwan zai iya zuwa da ambaliya.

Za a iya fuskantar walkiya da tsawa mara karfi yayin da zabga ruwa a wadannan jihohi.

Barazanar ambaliyar ruwan sama

Jihohin da ruwan zai iya yi sanadiyyar ambaliya sun hada da; Ribas, Delta, Bayelsa, Akwa Ibom da kuma Kuros Riba a yankin kudancin Najeriya.

A Arewa kuma NiMet ta kawo: Yobe, Binuwai, Jigawa, Kano, Katsina, Zamfara da Sakkwato.

Neja, Borno, Bauchi da Kaduna su na cikin inda hukumar ta ke ganin za ayi ruwa kadan ko kuma ba za a samu ba gaba daya a ‘yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Bayan Cire Tallafin Fetur. Tinubu Ya Waiwayi Ma’aikata, Ya Koka Kan Albashin da Ake Biya

Jerin jihohin da ruwan zai shafa:

1. Sakkwato

2. Zamfara

3. Katsina

4. Kano

5. Bauchi

6. Kaduna

7. Filato

8. Oyo

9. Kogi

10. Nasarawa

11. Binuwai

12. Adamawa

13. Taraba

14. Kuros Riba

15. Imo

16. Ondo

17. Edo

18. Delta

19. Bayelsa

20. Ribas

Satar da ake yi a Najeriya

Ku na da labarin cewa satar man fetur ta jawo gagarumar asara ga ƙasar nan har ta kai a cikin shekara 11 an yi asarar $46bn (N16.25trn)

Tajudeen Abbas a matsayinsa na shugaban majalisar wakilai ya bayyana babbar matsalar da satar arzikin ta ke jawowa ga ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng