‘Yan Majalisa Sun Gayyaci Ministoci 2 Kwanaki Kadan Bayan Tinubu Ya Nada Su
- ‘Yan majalisar wakilan tarayya sun bukaci zama da wasu manyan jami’an gwamnatin tarayya
- Wani kwamitin bincike da aka kafa ya aika sammaci ga ministocin tattalin arziki da na masana’antu
- Hon. Afam Ogene ya ce su na son gano inda kudi su ka shige da sunan tsare-tsaren zirga-zirga
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Kwamitin majalisar wakilan tarayya ya gayyaci wasu daga cikin ministocin gwamnatin Najeriya, Wale Edun da kuma Doris Uzoka-Anite.
The Cable ta kawo rahoto cewa kwamitin ya na binciken aikin tsarin zirga-zirgan motocin jama’a da gwamnati ta fara, amma ba a iya gamawa ba.
Kwamitin ya gayyaci Akanta Janar na gwamnatin tarayya, Oluwatoyin Madein a kan batun, ya ce ba da wasa ya dauki gayyatar da aka aika ba.
Majalisar tarayya ta gayyaci OHCSF
Wata jami’ar gwamnatin tarayya da kwamitin ya aikawa goron gayyata ita ce shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Folasade Yemi-Esan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kwamitin majalisar, Afam Ogene ya aika sammacin ne a ranar Laraba bayan sauraron bayanan jama’a da majalisar tayi a garin Abuja.
Aikin da kwamitin Majalisar za ta yi
Kwamitin ya ce an yi ta kirkiro tsare-tsare da nufin saukawa zirga-zirga a Najeriya, amma a dalilin rashin kula, duk sun gagara yin aiki har zuwa yau.
Ogene ya ce ana bukatar wadanda aka gayyata su gabatar da bayanan da za a bukata a gaban kwamitin domin jin abin da ya hana tsare-tsaren aiki.
Kamar yadda aka rahoto ‘Dan majalisar ya ce kwamitinsa a shirye yake ya ji yadda dukiyoyi su ka shiga aljihun tsirarun mutane domin a karbo su.
Baya ga haka, za a aika goron gayyata zuwa ga shugaban bankin gina abubuwan more rayuwa domin ya halarci zaman da za ayi da sauran jami’an.
Wale Edun da Uzoka-Anite sun zama ministocin Bola Tinbu ne a watan Agusta bayan majalisar dattawa ta tantance su tare da sauran wasu.
Ministocin Tinubu a ofis
Kun ji yadda David Umahi ya shirya zai yaki da ‘yan kwangila da kamfanonin gida da su ke saida buhun siminti da tsada duk da sun samu dama.
Daga gyara zama a kan kujera, Festus Keyamo ya soke matakan da Muhammadu Buhari ya dauka duk da ya na cikin tsohuwar gwamnatin APC.
Asali: Legit.ng