Atiku Ya Yi Martani Ga Kashim Shettima Kan Batun Yi Masa Ritaya
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abuɓakar ya yi martani ga Kashim Shettima kan batun yi masa ritaya a siyasa
- Ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa lokacin ritayarsa a siyasa bai yi ba tukunna
- Atiku ya kuma musanta rahotannin cewa ya taya shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar nasarar da ya samu a kotun zaɓe
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa lokacin ritayarsa a siyasa bai yi ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya ce zai siya masa tumakai da awakai domin ya yi ritaya daga siyasa, cewar rahoton Daily Trust.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya sha alwashin cigaba da bayar da tashi gudunmawar wajen ganin dimokuraɗiyya ta samun wajen zama a ƙasar nan.
Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi
Atiku, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ta hannun mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya bayyana cewa lokacin ritayarsa a siyasa bai yi ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ba zai yi ritaya ba sannan a maimakon hakan zai cigaba da kasancewa cikin gwagwarmayar ganin dimokuraɗiyya ta samu wajen zama a ƙasar nan." A cewar Ibe.
Atiku bai ta ya Tinubu murna ba
Sanarwar ta kuma ƙaryata rahotannin da ke cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ta ya shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, murna kan nasarar da ya samu a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.
A cewar Vanguard, wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Atiku ba zai iya aminta da 'yn fashin zabe ba saboda yin hakan zai zama fyade ga burin ‘yan Najeriya da suka kwashe shekaru suna gwagwarmayar tabbatar da sahihin zaɓe."
"Idan sun gamsu cewa nasarar da suka samu tana da inganci, ina ganin ba buƙatar su tsaya suna yi wa yan adawa zagon ƙasa wajen taya su murna ta hanyar labaran karya."
Tinubu Zai Cigaba Da Nasara Kan Atiku, Obi - Hamzat
A wani labarin na daban kuma, shugaban Connected Development (CODE) Hamzat Lawal ya yi tsokaci kan hukuncin kotun zaɓen shugaban ƙasa.
Hamzat ya bayyana cewa idan har ba haɗaka Atiku da Peter Obi suka yi ba, ba za su iya yin nasara akan Shugaba Tinubu ba a zaɓen 2027 mai zuwa.
Asali: Legit.ng