Kotun Zabe: Alkalai Sun Caccaki Lauyoyin Peter Obi Kan Rashin Hujjoji

Kotun Zabe: Alkalai Sun Caccaki Lauyoyin Peter Obi Kan Rashin Hujjoji

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yi hukunci kan ƙararrakin da aka shigar a gabanta ana ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu
  • A yayin da kotun take yanke hukuncinta, ɗaya daga cikin alƙalan kotun ta caccaki lauyoyin Peter Obi na LP kan rashin kawo gamsassun hujjoji
  • Mai shari'a Monsurat Bolaji-Yusuf ta nuna cewa lauyoyin ba su kawo ƙwararan hujjoji a gaban kotun ba kan ƙarar da Peter Obi ya shigar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a jiya Laraba, 6 ga watan Satumba, ta zartar da hukuncinta kan ƙarar da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa LP da Atiku Abubakar na PDP suka shigar kan Shugaba Tinubu.

Peter Obi da Atiku suna ƙalubalantar nasarar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa, na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Dandazon Mutane Sun Yi Zanga-Zanga a Kotun Zaɓe, Sun Aike da Muhimmin Saƙo Ga Atiku da Obi

An caccaki lauyoyin Peter Obi a kotu
Kotu ba ta ji dadin yadda lauyoyin Obi suka kasa kawo hujjoji ba Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Da kotun take yanke hukuncinta kan ƙarar da Peter Obi ya shigar, ta nuna takaicinta kan yadda lauyoyinsa suka kasa kawo ƙwararan hujjojin da za su goyi bayan ƙalubalantar nasarar da Shugaba Tinubu ya samu.

Lauyoyin Obi ba su da hujja, kotu

Mai shari'a Monsurat Bolaji-Yusuf ta yi nuni da cewa a maimakon lauyoyin su kawo ƙwararan hujjoji, sai suka saki jiki suna jin cewa wanda su ke karewa ne ya lashe zaɓen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin wani bidiyo da @thecableng ta sanya, mai shari'ar ta bayyana cewa:

"Masu shigar da ƙara ba su fahimci baya nan wanda ake ƙara ba ko kawai dai suna ji a jikinsu sun lashe zaɓen ba tare da kawo ƙwararan hujjoji bai, sannan ba su damu da kawo waɗannan ƙwararan hujjojin a gaban wannan kotun ba."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Peter Obi Ya Yi Nasara Akan Shugaba Tinubu Da Shettima a Kotun Zabe

"Suna tsammanin kotu ce za ta je ta samo musu hujjoji daga titi ko kasuwa? ko ta ji tsoron barazanar da ake mata a soshiyal midiya. Ba haka kotu take ba."

Peter Obi Ya Yi Nasara a Kotu

A wani labarin na daban, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ta ƙi amincewa da buƙatun APC da Shugaba Tinubu kan zama ɗan jam'iyar Labour Party (LP).

Kotun ta kuma ƙi amincewa da buƙatar APC na yin fatali da ƙarar Peter Obi, saboda bai yi haɗaka da Atiku Abubakar wajen shigar da ƙarar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng