Yadda Abba Gida Gida Ya Yi wa Kanawa Rabon Kayan Tallafin Tsadar Man Fetur

Yadda Abba Gida Gida Ya Yi wa Kanawa Rabon Kayan Tallafin Tsadar Man Fetur

  • Marasa hali da masu karamin karfi sun ci moriyar rabon kayan tallafin da aka yi a jihar Kano
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi rabon buhunan hatsi baya ga na’urorin aikin gona da manoma
  • Mata sun samu kananan dabbobi da Abba Gida Gida ya raba domin kiwo a kauyukan Kano

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Gwamnan jihar Kano ya sanar da rabon kayan tallafi ga masu bukata a sakamkon janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon ne a ranar Litinin kamar yadda ya yi alkawari bayan ya karbi kason jiharsa daga gwamnatin kasa.

Mai girma Gwamnan ya yi rabon kananan buhunan shinkafa 273,460 da na masara 160, 000 ga marasa karfi da ke kananan hukumomin da ke jihar.

Aba Gida Gida
Gwamnan Kano, Abba Gida Gida Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

An samu tallafi a ko ina a Kano?

Kara karanta wannan

An Dawo da Tallafin Fetur, Gwamnati Ta Lallaba Ta Na Biyan Biliyoyin Kudi a Boye

Hassan Sani Tukur wanda ke taimakawa Abba Yusuf a kafafen sadarwa na zamani ya ce rabon kayan tallafin ya ratsa duka mazabu 484 da ke Kano.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta fahimci a kowace mazaba za a raba kilo 5650 na shinkafa da kilo 3330 na masara.

Su wa za su amfana da rabon?

Wadanda za su amfana da rabon kayan da za ayi su ne manoma, gidajen marayu, masu fama da nakasa, tsangayoyi da makarantun musulunci.

Sannan akwai kananan ma’aikatan gwamnati, gidajen gyaran hali da wasu daidaikun asibitoci a lokacin da litar man fetur ya zarce N600.

Manoma da matan kauye sun amfana

Da yake bayani a Twitter, Hassan Tukur ya ce matan karkara sun samu raguna da awaki sama da 2, 500 da za su yi kiwon da za su dogara da shi.

Kara karanta wannan

Bayan Cire Tallafin Fetur. Tinubu Ya Waiwayi Ma’aikata, Ya Koka Kan Albashin da Ake Biya

Baya ga haka, Gwamnan da aka fi sani da Abba Gida Gida ya bada injinan casar shinkafa ga kananan manoma, mutane 6000 su ka amfana.

A bangaren noman rani, gwamnatin Kano ta yi rabon na’urorin ban ruwa 2, 050 a makon nan.

Abba Gida Gida ya sanar da hakan a shafukan sada zumunta. Ana sa ran hakan ya rage kukan da ake yi na tsadar rayuwa saboda tashin man fetur.

Magana da Hadimin Gwamnan Kano

Hassan Sani Tukur a matsayinsa na mai taimkawa gwamnan Kano a kafofin sadarwa na zamani ya ce tallafin zai taimakawa gidaje 500, 000.

Bayan haka, hadimin ya kara da cewa kananan manoma da matan da ke kauyuka jihar Kano za su amfana da iri, kayan aiki da dabbobin kiwo.

Burin hakan a cewar Hassan Tukur shi ne a kawowa al’umma sauki musamman marasa galihu.

Tinubu ya koka da albashin ma'aikata

A duk lokacin da aka ba shi adadin ma’aikatan da ke karbar albashin gwamnati, an ji labari Bola Tinubu ya ce ya na firgita sosai saboda yawan kudin.

Kara karanta wannan

Kwanaki 100 Kan Mulki: Tarun Matsaloli 3 Da Ke Hana Shugaba Tinubu Sakewa Tun Bayan Hawanshi Mulki

Shugaba Bola Tinubu ya na kukan inda za a samu kudin da ake bukata wajen gina abubuwan more rayuwa idan ma'aikata su na cinye kudin-shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng