Jimami Yayin Da Sheikh Giro Argungu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Al'ummar Musulmi na cikin jimami bayan samun labarin rasuwar shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Giro Argungu
- Giro Argungu ya rasu a yau Laraba 6 ga watan Satumba a Birnin Kebbi bayan fama da jinya
- Shugaban kungiyar Izalah ta kasa, Sheikh Bala Lau da Sakatarensa Kabiru Gombe sun tabbatar da rasuwar tasa a yammacin yau
Jihar Kebbi - Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Giro Argungu ya riga mu gidan gaskiya.
Allah ya karbi rayuwar Sheikh Abubakar Giro a yammacin yau Laraba 6 ga watan Satumba.
Waye ya sanar da rasuwar Sheikh Giro?
Shugaban kungiyar Izalah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a yau Laraba 6 ga watan Satumba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Giro kamar yadda Sheikh Kabiru Gombe ya wallafa a shafinsa na Facebook ya rasu bayan 'yar gajeriyar jinya a Birnin Kebbi.
Kabiru Gombe ya ce za a sallaci mamacin a gobe Alhamis 7 ga watan Satumba.
Yaushe za a sallaci Sheikh Giro?
Kamar yadda aka wallafa a shafinsa na Facebook za a sallaci marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu a gobe Alhamis 7 ga watan Satumba.
Majiyar ta ce za a yi sallar marigayin ne da misalin karfe 2:00 na rana a garin Argungu da ke jihar Kebbi.
Za a gabatar da sallar jana'izar a masallacin Idin Sarki da ke garin Argungu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a jiya ma kafin rashin lafiyar ta iske shi, marigayin ya yi karatu tsakanin Mangariba zuwa Isha.
Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu ya na da shekaru 60 a duniya, an haifi marigayin a ranar 3 ga watan Satumba ta shekarar 1963.
Bidiyoyi Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ganduje, Keyamo, Bala Mohammed Da Sauransu Ke Likimo a Kotun Zaben Shugaban Kasa
Giro ya bai wa addinin Musulunci gudumawa ta fannoni da dama wanda hakan ya sa ya zama daga cikin manyan malamai a kasar.
Barayi Sun Hallaka Shahararren Malamin Addini A Gombe
A wani labarin, barayi sun yi ajalin shahararren malamin addinin Musulunci mai suna Sheikh H. Musa a jihar Gombe.
Sheikh Musa wanda aka fi sani da Albanin Kuri ya rasa ransa bayan barayi sun kai masa farmaki.
Yanzu haka rundunar 'yan sanda a jihar ta bazama neman wadanda su ka aikata wannan aika-aika a birnin Gombe.
Asali: Legit.ng