Ku Yi Hakuri Tinubu Ya Dawo Daga Indiya, Zamu Warware Komai, Lalong Ga NLC
- Simon Lalong ya bayyana cewa da zaran shugaba Tinubu ya dawo daga Indiya za a warware ƙorafin ƙungiyar NLC
- Ministan kwadago da samar da ayyukan yi ya ce har yanzu bai samu sanarwan shiga yajin aiki a hukumance daga NLC ba
- NLC ta fara yajin aikin ranar Talata kuma ta ce wannan somin taɓi ne da ke nuna alamun zata shiga mafiyin shi nan gaba
FCT Abuja - Simon Lalong, Ministan Kwadago da samar da ayyuka ya roki Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta maida wuƙar kube har sai Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya dawo daga Indiya.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa shugaba Tinubu na ƙasar Indiya yanzu haka, inda zai halarci taron shugabannin ƙasashen G-20 a ranakun 9 da 10 ga watan Satumba.
A ranar 1 ga watan Satumba, shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya sanar da cewa ƙungiyar zata tsunduma yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu daga ranar Talata kan wahalhalun da suka biyo bayan cire tallafin man Fetur.
Haka nan kuma a ranar Litinin da ta gabata, Lalong ya yi kira da ƙungiyar NLC da ƙawayenta su dakatar da shirinsu na tafiya yajin aikin gargaɗi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ministan ya bayyana cewa matakin ka iya zama cikas ga nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu tun bayan karɓan mulkin Najeriya.
Lalong ya buƙaci NLC ta bari Tinubu ya dawo daga India
Da yake jawabi a cikin shirin NTA, Ministan ya tabbatar wa NLC cewa duka ƙorafinsu da ya sa suka shiga yajin aiki za a warware su idan Tinubu ya dawo Najeriya.
A ruwayar Premium Times, Lalong ya ce:
"Har yanzu ban samu sanarwar yajin aikin ba a hukumance, sai dai naga ana yi kawai. A cewar NLC, yajin aikin gargadi na kwanaki biyu somin taɓi ne na shiga yajin aikin kwanaki 14.”
“Kafin wannan lokaci, da zaran shugaban ya dawo daga Indiya, na tabbata da yawa daga cikin batutuwan da aka tabo, na yi alkawarin za mu magance su kafin kwanaki 14."
"Saboda haka babu bukatar shiga yajin aikin nan na kwanaki biyu domin manufar shiga yajin aikin shi ne, ba a kula da su ba."
Ana Yajin Aiki, Gwamna Bago Ya Amince da Bai Wa Kungiyar NLC Motocin Shinkafa
A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Neja ya amince a bai wa ƙungiyar kwadago NLC Tirela biyu na shinkafa domin rage raɗaɗin cire tallafin fetur.
Ya ƙara da cewa Naira miliyan N110 da gwamnatinsa ta amince a bai wa NLC a farko, an ba su ne a matsayin kuɗin aikin sa ido kan rabon kayan tallafi a faɗin gundumomi 274 na jihar Neja.
Asali: Legit.ng