Gwamnati Ta Lallaba Ta Na Biyan Biliyoyin Kudi a Boye da Aka Dawo da Tallafin Fetur
- An koma gidan jiya a Najeriya domin har yanzu gwamnatin tarayya ta na saukaka farashin fetur
- NNPC ta ke da dawainiyar wahalar da ake yi domin kusan babu wadanda ke shigo da man fetur
- Idan aka bar farashi a hannun ‘yan kasuwa, sai an koma saida litar fetur a kan akalla N818 a yau
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Akwai alamun da ke nuna gwamnatin tarayya ta cigaba da biyan tallafin man fetur, bayan Bola Ahmed Tinubu ya soke tsarin.
Rahoto da aka samu a The Guardian ya ce gwamnatin Najeriya na amfani da kamfanin NNPP da aka cefanar wajen hana farashi tashi.
Kusan har yanzu NNPC kadai ke da wuka da nama wajen sha’anin man fetur a Najeriya.
NNPC ta na tafka asarar kawo fetur?
Binciken da aka yi ya nuna an yi asarar Naira biliyan 318 a kamfanin NNPC wajen shigo da man fetur duk da ana cewa an tara kudi.
Karauniya Yayin Da Aka Sanar Da Sabon Farashin Gas Sabanin Yadda Tinubu Ya Yi Alkawari A Baya, Bayanai Sun Fito
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ana biyan wadannan kudi ne a boye bayan Bola Tinubu ya sanar da nasarorin da aka samu a sakamakon cire hannun gwamnatinsa.
Bayan an yi canjin gwamnati a kasar ne Huub Stokman na NNPC ya zama shugaban kungiyar MOMAN na manyan dillalan man fetur.
Ana karya Dala ga masu fetur
Gwamnatin Bola Tinubu ta na yi wa ‘yan kasuwan rangwame ta hanyar ba su dala a farashi mai rahusa, bayan an daidaita farashin.
Duk da NMDPRA ta ba kamfanoni lasisin dauko fetur daga kasashen waje, ‘yan kungiyar MOMON ba su samun dala da araha.
Fetur ya kara tsada a kasuwa
Lissafin da aka yi ya nuna a karshen Agusta, kudin kowane litar man fetur ya karu da 19.88% zuwa kimanin N617 a kasuwannin duniya.
Baya ga haka kafin ya iso gidajen mai sai an biya kudin dako a ruwa da na jigila daga tasohihi, amma har yau farashi bai motsa ba.
Sai da Dalar Amurka ta zarce N900 a hannun ‘yan canji, wanda hakan ya nuna babu abin da zai hana fetur kara tashi daga N615-N620.
Da gwamnati ba ta fito da wannan dabara ba, farashin man fetur zai zama tsakanin N818 da N833 domin a N728.64 ya ke isowa Najeriya.
Meya hana Buhari cire tallafin fetur?
Kwanakin baya an ji tsohon shugaban Najeriya ya ce bai janye tallafin an fetur ba ne saboda Bola Tinubu ya iya lashe zaben da aka yi.
Haka aka yi a gwamnatin Muhammadu Buhari inda NNPP ta rika asara a maimakon aka rika batar da makudan kudi a kan ‘yan kasuwa.
Asali: Legit.ng