Asari Dokubo Ya Aike Da Matasa Zuwa Kotun Zaben Shugaban Kasa
- Yaran Asaro Dokubo, tsohon shugaban tsagerun Neja Delta sun dira harabar kotun zaɓen shugaban ƙasa a Abuja
- Matasan ɗauke da alluna sun je kotun ne domin nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- A yau ne dai kotun zaɓen za ta yanke hukuncinta kan ƙararrakin da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar na ƙalubalantar nasarar Tinubu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Tsohon shugaban tsagerun yankin Neja Delta, Asari Dokubo, ya tattaro matasa ɗauke da alluna a safiyar ranar Laraba sun dira harabar kotun ɗaukaka ƙara, rahoton PMnews ya tabbatar.
Matasan dai sun dira harabar kotun ne domin nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a yayin da ƴan Najeriya ke jiran hukuncin da kotun za ta yanke a shari'ar zaɓen shugaban ƙasa na ranar, 25 ga watan Fabrairun 2023.
Menene abin da matasan suka je yi a kotun
Matasan dai suna sanye ne da baƙaƙen kaya da jajaye waɗanda aka sanya sunan Asari Dokubo a jiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan suna ɗauke da alluna yayin da su ke rera waƙoƙi da yin raye-raye.
Saƙonnin da ke jikin allunan na cewa:
"Ƴan Neja Delta na goyon bayan nasarar da ƴan Najeriya sama da miliyan 200 suka ba Shugaba Tinubu."
"Shugaba Tinubu yana son Neja Delta' da mun gode Tinubu bisa dawo da ma'aikatar Neja Delta".
Kotu za ta yanke hukunci yau Laraba
A ranar Litinin, 4 ga watan Satumba, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ta tsayar da yau Laraba, 6 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta yanke hukuncinta kan shari'ar zaɓen shugaban ƙasa.
Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party (LP), na iƙirarin cewa su ne suka lashe zaɓen shugaban ƙasan ba Shugaba Tinubu ba
Abubakar ya samu ƙuri'u 6.9m sannan Peter Obi ya samu ƙuri'u 6.1m a zaɓen shugaban ƙasar na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Fasto Ta Bayyana Zabin Allah a Tsakanin Tinubu, Atiku Da Obi
A wani labarin kuma, fasto Christiana Eunice wacce ta kafa cocin Covenant Of God Church Praise Sacrament, ta bayyana zaɓin Allah a tsakanin Tinubu, Atiku da Ƙeter Obi.
Fasto Eunice ta bayyana cewa Peter Obi shi ne wanda Allah ya zaɓa domin ya kawo sauyi mai inganci a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng