SSS Ta Cafke ‘Yan Uwan Tsohon Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa

SSS Ta Cafke ‘Yan Uwan Tsohon Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa

  • Binciken da hukumar SSS ta ke yi wa dakataccen shugaban EFCC ya kai ga wasu ‘yanuwansa
  • Bayan amsa tambayoyi, an karbi wasu motoci daga hannun ‘yanuwan Mista Abdulrasheed Bawa
  • An tsare babbar hadima da kuma Lauyan shugaban hukumar yaki da rashin gaskiya a Najeriya

Abuja - Ana zargin jami’an SSS sun gayyaci wasu ‘yanuwan shugaban hukumar EFCC na kasa da aka dakatar, Abdulrasheed Bawa.

Dalilin kiran wadannan mutum biyu da jami’an tsaro su ka yi shi ne yi masu tambayoyi, Daily Nigerian ta fitar da rahoton a makon nan.

Hakan na zuwa ne bayan Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa a watan Yuni.

Abdulrasheed Bawa
Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

An cigaba da rike Abdulrasheed Bawa

Makonni biyu da hawa mulki, Mai girma shugaban kasa ya tsaida shugaban hukumar da nufin gudanar da bincike a kan wasu zargi.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Kama Jami'an Gwamnati Da Ke Karkatar da Tallafin da Ake Raba Wa Talakawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har zuwa yanzu Bawa ya na tsare yayin da mutane da kungiyoyin fararen hula su ke kira ga gwamnati ta sake shi ko dai ta kai shi gaban kotu.

SSS v 'Yanuwan Abdulrasheed Bawa

Rahoton ya ce wadanda su ka shiga hannun jami’an tsaro masu fararen kaya su ne Yazid Bawa wanda shi ma ya na aiki da hukumar EFCC.

Sannan an kira Bashir Bawa, wani jami’i a hukumar NCC mai kula da harkoki sadarwa. Zuwa yanzuEFCC ba ta yi magana a kan batun ba.

SSS ta karbe wata mota wanda harsashi bai ratsa ta a hannun ‘yanuwan shugaban hukumar da ke yaki da alhakin rashin gaskiya a Najeriya.

Har ila yau, an ce an karbe wata sabuwar motar da kamfanin Mercedes-Benz ta kera a hannunsu.

Ana cigaba da binciken EFCC

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Sako Dakataccen Karamar Hukumar Jihar APC da Ta Tsare, Bayanai Sun Fito

Abin bai tsaya nan ba, Hadiza Gamawa wanda ita ce shugaban ma’aikatan da ke ofishin shugaban EFCC ta sha tambayoyi a hannun DSS.

Mai ba Bawa shawara kan sha’anin shari’a, U.U. Buhari ya na cikin wadanda aka yi wa tambayoyi da nufin gano gaskiyar tulin zargin da ake yi.

N1bn sun yi kafa a NNPP?

A bangaren siyasa, an ji labari NNPP za ta yi bincike a kan yadda aka yi fatali da fiye da Naira biliyan daya da aka samu wajen saida fam a zabe.

An yanke shawarar a gayyato hukumomin tsaro su yi binciken asusun jam’iyyar NNPP a dalilin rikicin da ake yi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng