Ministocin Najeriya 4 da Su ka Fara Jawo Rudani Daga Shigansu Ofis Zuwa Yau

Ministocin Najeriya 4 da Su ka Fara Jawo Rudani Daga Shigansu Ofis Zuwa Yau

  • Bola Tinubu ya nada ministocinsa a ranar 21 ga watan Agusta, har yanzu ba su yi wata a ofis ba
  • Zuwa yanzu akwai wadanda labarin ayyukansu ya zagaya duk da ba su wuce makonni a mulki ba
  • Akwai wadanda lamarinsu ya na neman jawo badakala, wasu kuma sun dauko aiki a gabansu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A wannan rahoton, Daily Trust ta kawo jerin wasu ministoci da sunayensu ya rika karada gidajen jaridu ko da ba su dade a kan mulki ba.

Babu mamaki akwai wasu ministocin tarayyar da rahoton nan bai iya kawo maku su ba.

Ministocin Najeriya
Taron Ministoci na FEC Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

1. Minsitar al'adu - Hannatu Musawa

Kowa ya ji yadda ake ta hayaniya da Hannatu Musawa a game da batun NYSC, tun a shekarun baya aka fara maganar ba ta yi bautar kasa ba.

Kara karanta wannan

Wike Ya Bada Umarnin Ruguza Shaguna Yayin da Ake Cigaba da Rusau a Abuja

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abin ya kara jawo magana da aka ji yanzu ta ke yin bautar kasa alhali kuma ta na minista.

2. Minsitan Abuja - Nyesom Wike

Zuwa yanzu labarin Nyesom Wike ya karada ko ina a sakamakon umarnin da ya ke ba jami’an hukumar FCTA na ruguza gine-gine a Abuja.

Baya ga rusa wasu gine-gine da shaguna a birnin tarayya, Wike ya shirya yaki da ma’aikatansa.

3. Minsitan jiragen sama - Festus Keyamo

Zamansa minista ke da wuya sai aka ji Festus Keyamo, SAN ya bada umarnin dakatar da aikin samar da kamfanin jirgin saman Nigeria Air.

Zuwa yanzu ya soke jinginar da wasu tashoshin tashin jirgi da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi a lokacin ya na ministan kwadago.

4. Minsitan ayyuka - David Umahi

Daga zamansa ministan ayyuka, David Umahi ya nuna ba zai yarda da yadda ake kwangilolin ayyuka ba, har ana batun za su raba gardama a kotu.

Kara karanta wannan

Bayan Cire Tallafin Fetur. Tinubu Ya Waiwayi Ma’aikata, Ya Koka Kan Albashin da Ake Biya

Sanata Umahi ya nuna ba zai yarda da yadda siminti ya yi tsada ba, ya ce dole a rage farashi.

Rayuwa bayan mulki

Kwanan nan Madam Lauretta Onochie ta sauka daga matsayinta a hukumar NDDC bayan ta yi aiki a matsayin hadimar Shugaba Muhammadu Buhari.

Ku na da rahoto wani fai-fen bidiyo ya nuna ana rikici da hadimar shugaban kasar a wani gida a Landan a Birtaniya, hakan ya jawo ta fito ta yi jawabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng