Dama Na San Bai San Tattalin Arziki ba – Obasanjo Ya Kuma Ragargazar Buhari
- A cewar Olusegun Obasanjo, ya na da masaniyar Muhammadu Buhari bai fahimci tattalin arziki ba
- Tsohon shugaban Najeriyan ya soki yadda gwamnatin baya tayi facaka, ta bar kasar nan da tarin bashi
- Obasanjo ya yi sanadiyyar yafe bashin da kasar nan ta karba, ya ce a yau ba za a yafewa Najeriya ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya a lokacin mulkin soja da na farar hula, ya yi shekaru fiye da 10 a kan karaga, ya san kan kasar nan.
A wata hira ta musamman da ya yi da The Cable, Cif Olusegun Obasanjo ya yi maganar shugabanci, lantarki, tattalin arziki da dai sauransu.
Tsohon shugaban na Najeriya ya zargi Muhammadu Buhari wanda ya yi mulki tsakanin 2015-2023 da taimakawa wajen ruguza tattalin arziki.
Buhari ya sa bashin Najeriya ya dawo danye
Obasanjo ya na ganin gwamnatin Buhari ta rika facaka da dukiya, ya ce a yanzu an shiga matsala bayan Bola Ahmed Tinubu ya karbi ragama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin da aka yafewa Najeriya bashin da ake bin ta a mulkin Obasanjo, da Buhari ya karbi mulki sai ya rika laftowa gwamnati bashin kudi.
Tsohon shugaban ya ganin a duniyar yau, babu wanda zai yafewa Najeriya bashin da ke wuyanta.
"Ku na tunanin akwai wani wanda zai yafewa Najeriya bashin kudin da ta karbo aro a yau? Buhari ya rika kashe kudi da ganganci.
Na san Buhari bai fahimci tattalin arziki ba. Na rubuta wannan a cikin littafi na. Amma kuma ya rika yin facaka, ban san da wannan ba.
Ban san a yau wajen wa za ka je neman alfarma ba? Tinubu zai hadu da Justin Trudeau da Emmanuel Macron, ba za a magance matsalar ba.
- Olusegun Obasanjo
Da Buhari komai ya fi a biyan bashi
Kamar yadda ya shaidawa jaridar, rage adadin wadanda za su je taron majalisar dinkin duniya da Bola Tinubu ya yi ba zai sa komai ya canza ba.
Tsakanin 1999 da 2003 da Obasanjo ya yi mulki, gwamnati ba ta kashe duk kudinta wajen biyan bashi ba, akasin abin da gwmanatin APC ta ke yi.
Shekaru 8 Buhari ya na barna
Ku na da labari Muhammadu Sanusi II ya yi Allah-wadai da yadda gwamnatin da ta wuce ta rike tattalin arziki, ya ce an yi shekaru takwas a lalace.
Tsohon gwamnan na CBN kuma masanin ilmin tattalin ya zargi shugabannin da su ka bar mulki da rashin daukar shawarar kwararrun masana.
Asali: Legit.ng