Fasto Olukoya Ya Gargadi Mata Masu Ciko A Mazaunai Da Mama, Ya Ce Sun Shiga Tarkon Shaidan
- A zamanin nan da mu ke ciki ciko ko kari a mazaunai ko mama ya zama ruwan dare a wurin mata saboda burge mazaje
- Fasto Daniel Olukoya ya gargadi masu yin irin wannan aika-aika inda ya ce tabbas shaidan ya riga ya yi fitsari a kansu
- Ya ce irin wadannan mata ba su gamsu da halittar da ubangiji ya musu ba kuma shaidan ba zai bata lokacinsa a kansu ba
Jihar Legas – Shugaban cocin Mountain of Fire and Miracles Ministries (MFM), Fasto Daniel Olukoya ya tura gargadi ga mata masu yin ciko.
Faston ya ce duk macen da ta ke ciko a bayanta ko mama ta tabbata shedaniya kuma shaidan ya riga ya yi nasara a kanta.
Meye Faston ke cewa kan mata?
Ya ce shaidan ba zai bata lokaci ba kan irin wadannan saboda ya gama da su tun a karon farko, cewar Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Olukoya ya bayyana haka ne yayin huduba a cocinsa a jiya Lahadi 3 ga watan Satumba.
Ya kara da cewa wadanda ke ciko sun nuna cewa ba su ji dadin yadda ubangiji ya haliccesu ba shi yasa su ke kari.
Wane gargadi Faston ya yi wa mata?
Ya ce:
“Mafi yawan mabiya abin takaici sun zamo marasa amfani wanda shaidan ba zai bata lokacinsa a kansu ba saboda ya kama su.
“Idan kina mace kika yi kari ko ciko a bayanki ko mama, kin riga kin lalace, kina fadawa ubangiji cewa ba ki gamsu da halittarki ba.
“Ko shaidan ba zai bata lokaci a kan irin wadannan ba saboda ya riga ya kama su tun da wuri.”
A zamanin nan da mu ke ciki ciko ko karin a mazaunai ko mama ya zama ruwan dare ga mata saboda burge mazaje.
Wasu har tiyata ake musu don karin mazaunai da mama inda ake cire wasu sassa na jikinsu don cikatawa a mazaunai, TheCable ta tattaro.
Fasto Kingsley Ya Yi Martani Kan Shari'ar Peter Obi Da Tinubu
A wani labarin, yayin aka sanar da ranar yanke hukuncin na zaben shugaban kasa, wani shahararren Fasto ya bayyana abin da zai faru.
Fasto Kingsley Okwuwe na Revival and Restoration Mission ya ce dan takarar shugaban kasa a jam’iyar Labour, Peter Obi zai karbi mulkin da aka kwace masa.
Asali: Legit.ng