Kungiyar Ohanaeze Ta Bayyana Abin Da Zai Faru Da Shugaba Tinubu Idan Kotu Ta Umarci a Sake Zabe
- Tsagin Chidi Ibeh na ƙungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa ƴan Arewa ba su jindaɗin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Ohanaeze ta bayyana cewa akwai yiwuwar yankin Arewacin Najeriya ya juya wa Tinubu baya idan kotu ta ce a sauya zaɓe
- Ƙungiyar Inyamuran ta bayyana cewa Arewacin Najeriya na tsoron sake sauya fasalin ƙasar nan
Jihar Enugu - Tsagin Chidi Ibeh na ƙungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo, ta bayyana cewa akwai yiwuwar yankin Arewacin Najeriya ya juyawa Shugaba Tinubu baya idan kotun zaɓe ta bayar da umarnin a sake zaɓe.
A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba, Okechukwu Isiguzoro, sakataren ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, ya yi iƙirarin cewa ƴan siyasar Arewa ba su gamsu da salon kamun ludayin Shugaba Tinubu ba.
Da Dumi-Dumi: Hukumar DSS Ta Bankado Shirin Tayar Da Tarzoma a Kasa, Ta Magantu Kan Masu Hannu a Ciki
"Arewa ta kaɗu kan shugabancin Tinubu": Ohanaeze
Ƙungiyar ta bayyana cewa manyan ƴan siyasar yankin na nan na jira kotu ta yi hukuncinta domin aiwatar da shirin da suka shirya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rahoton The Guardian, ƙungiyar Inyamuran ta gargaɗi Tinubu kan haɗarin da ke tafe.
Ohanaeze ta bayyana cewa juyin mulkin kwanan nan da aka yi a ƙasashen Nijar da Gabon gargaɗi ne kan zaɓen maguɗi da shugabanci mara kyau a nahiyar Afirika
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Yankin Arewacin Najeriya ya kaɗu kan kamun ludayin shugabancin Bola Tinubu da yiwuwar sauya fasalin ƙasa, da naɗa jajirtaccen ɗan Kudancin Najeriya a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja."
"Abu mafi muhimmanci shi ne duk wasu muƙamai masu gwaɓi an miƙa su ga yankin Ƙudi maso Yamma wanda hakan ya sanya Arewacin Najeriya shiga cikin ruɗani kan tunanin abin da zai faru a gaba."
Kotu Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci
A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncinta, kan shari'ar zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.
Kotun ta bayyana cewa a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, za ta zartar da hukuncinta kan ƙararrakin da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar na ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng