Kamfanin Siminti Na Dangote Ya Biya Gwamnatin Tarayya Kudin Haraji Naira Biliyan 412 Cikin Shekaru 3 Kacal
- Gwamnatin Tarayya na karbar makudan kudade daga kamfanonin Dangote a Najeriya
- Kamfanin Dangote na siminti kadai ya biya makudan kudade har Naira biliyan 412 a shekaru uku
- Dangote ya shawarci mutane da kamfanoni su ke biyan haraji don samun ingantacciyar rayuwa daga gwamnati
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Kamfanin siminti na Dangote ya biya akalla Naira biliyan 412.9 kudin haraji ga Gwamnatin Tarayya a cikin shekaru uku.
Jimillar Naira biliyan 97.24 kamfanin ya biya a 2020 da kuma Naira biliyan 173.93 a 2021 yayin da ya biya Naira biliyan 141.69 a 2022.
Nawa Dangote ke biyan kudin haraji ga gwamnati?
Dukkan wadannan makudan kudade an biya su ne daga kamfani guda daya kacal karkashin Aliko Dangote, cewar Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Labari Mai Dadi Yayin da Gwamnan Arewa Zai Kashe Biliyan 3.7 Wajen Siyawa Al’ummar Jihar Shinkafa Da Kayan Hatsi
Dangote ya tabbatar da cewa biyan haraji a kan lokaci kuma dai-dai dole ne a kan ko wane dan kasa idan ya na son ci gaba da girma.
Ya bayyana cewa gwamnati ba za ta iya samar da kayan more rayuwa ga al'umma ba sai da biyan kudin haraji.
Dangote ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta inganta biyan haraji a kasar inda ya yabi tsarin kaddamar da kwamitin shugaban kasa na kudade da haraji.
Meye Dangote ya ce kan biyan haraji ga gwamnati?
Ya ce:
"Duk lokacin da 'yan kasa su ka ga gwamnati na samar da abubuwan more rayuwa a cikin gida za su fara biyan kudin haraji.
"Inganta rayuwar al'umma musamman a bangaren ilimi da lafiya zai ba wa 'yan kasa damar biyan kudin haraji ba tare da fita kasashen waje ba."
Sauran kamfanoni da ke karkashin Aliko Dangote su na biyan makudan kudade na haraji a tsawon lokacin da ake magana, Daily Trust ta tattaro.
Lissafin makudan kudade na kamfanoni uku na Dangote sun kai Naira biliyan 114.39 a 2020 da Naira biliyan 187.17 a 2021 sai kuma Naira biliyan 172.15 a 2022.
Dangote Ya Karyata Karin Farashin Siminti A Najeriya
A wani labarin, Kamfanin siminti na Dangote ya karyata jita-jitar cewa ya kara farashin siminti a Najeriya fiye da sauran kasashe.
Ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya kan haka inda ya ce mafi yawanci farashin simintin ya fi sauki a kasashen Nahiyar Afirka ta Yamma kan sauran kasashe.
Asali: Legit.ng