Wasu ‘Yan Bindiga Sun Bude Wuta a Kan Titi, Sun Yi Awon Gaba da Mutane a Abuja
- Wasu matafiya sun shiga ha’ula’i a lokacin da su ke tafiya a kan hanyar Abuja-Lokoja a makon jiya
- ‘Yan bindiga sun tare hanyar, su ka shiga ruwan bindigogi, su ka tare motocin da su ka dauko fasinjoji
- Miyagun sun kammala ta’asarsu a jeji kafin ‘yan banga su iya kawowa matafiya dauki daga kauyuka
Abuja - Wasu da ake zargin masu yin garkuwa da mutane ne, sun budawa motoci wuta a kusa da kauyen Ochonyi a kan babban titin Abuja-Lokoja.
Rahoton da Daily Trust ta fitar ya tabbatar da cewa wadannan miyagu sun yi nasarar dauke fasinjoji da-dama da ke hanyar fita daga birnin tarayyar kasar.
Wani daga cikin wadanda masifar ta auka masu, Shedrack Jonathan ya shaida cewa ya shigo mota daga tashar Jabi a Abuja ne da niyyar tafiya Enugu.
An tare motoci da 7:30 a titin Abuja
A karshe Shedrack Jonathan ya shige daji domin ya kubuta da ran shi da aka tare motarsu da kimanin karfe 7:30 bayan sun wuce kauyen Omoko.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Matafiyin ya shaida cewa su na burmawa kan gangara a titin a yammacin Alhamis sai su ka ji harbin bindiga, nan ta ke motarsu ta juya ta nufi jeji.
Abin da su ka ji bayan nan shi ne wasu mutane dauke da bindigogi sun ingiza keyarsu zuwa jeji. Ana fama da rashin tsaro har cikin masallatai.
Bayan an shafe kusan kilomita guda ana tafiya a jeji, Jonathan ya samu damar sulalewa, ya bullo a wani kauye mai suna Aseni, a nan aka cece shi.
Matafiyin yake cewa ya ci karo da jami’an tsaron sa-kai, wadanda su ka kawo masa agaji bayan ya yi masu bayanin abin da ya faru da su a kan hanya.
'Yan bindiga sun tserewa 'yan banga
Wani ‘dan banga a yankin da ya yi magana ba tare da an kama sunansa ba, ya bada tabbacin cewa an dauke fasinjoji da-dama da aka tare motocinsu biyu.
A cewarsa, ‘yan bindigan sun harbe tayoyin motocin, hakan ya tilastawa direbobin hakura da tukin.
Kafin ‘yan banga su isa inda abin ya faru, ‘yan bindigan sun tasa keyar fasinjojin yayin da motocin ke titi, zuwa yanzu ‘yan sanda ba su ce komai ba
Sojoji a kan juyin mulki a Najeriya
Ana da labari cewa Manjo Janar Mohammed Takuti Usman ya fadawa jami'ansa cewa babu wani wurin zaman sojin da bai biyayya ga shugabannin kasa.
Janar Takuti ya ce idan soja ba zai iya yin da'a ba, ya tafi neman wani aiki dabam, ganin ana ta juyin mulki a Afrika, ya ce dole su zama sojoji masu biyayya.
Asali: Legit.ng