Shugaban Najeriya Tinubu Zai Shilla Kasar Waje Halartar Taron Shugabannin G-20
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Tinubu zai shilla kasar Indiya domin halartar wani taron shugabannin duniya
- An ruwaito yadda Tinubu ya samu gayyatar halartar wannan taro mai muhimmanci da za a yi nan ba da jimawa ba
- Rahoton ya kuma bayyana wadanda shugaban kasar zai tafi dasu zuwa kasar da ke nahiyar Asiya mai tarin jama’a da yawa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai shilla birnin New Delhi ta kasar Indiya ranar Litinin domin halartar taron shugabannin kasashen G-20, kamar yadda kakakinsa, Ajuri Ngelale ya bayyana, Channels Tv ta ruwaito.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Ngelale ya ce shugaban zai bar Abuja ne domin halartar taron a Indiya bisa gayyata ta musamman da firaministan kasar, Narendra Modi ya yi masa.
Ya kuma bayyana kadan daga abubuwan da Tinubu zai yi a wurin taron da kuma a gefensa idan ya samu damar halarta.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"A gefen taron, shugaban kasar zai halarta tare da gabatar da jawabai masu mahimmanci a ganawar shugabannin Najeriya da Indiya da kuma taron kasuwanci na Najeriya da Indiya."
Su wa za su halarci taron?
Ana sa ran taron zai samu halartar manyan jiga-jigai a fannin masana'antu da kamfanoni masu zaman kansu na Indiya, Najeriya, da kuma manyan jami'an gwamnati na kasashen biy, rahoton Tribune Online.
A taron na G20, ana sa ran shugaban na Najeriya zai bayyana ra'ayin Najeriya game da taken, ‘One Earth-One Family-One Future’ tare da mai da hankali kan hadin kan duniya da ake bukata don magance kalubalen da bil'adama da duniya ke fuskanta.
Shugaban zai tafi ne tare da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar; Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun; Ministan sadarwa, kirkire-kirkire, da tattalin arziki na zamani Bosun Tijani; da Ministar Masana'antu, Kasuwanci, da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite.
Tafiyar Tinubu zuwa kasar waje a baya
A wani labarin, Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya a ranar Asabar, 9 ga watan Yuli domin halartar taron ECOWAS da za ayi a kasar Guinea-Bissau.
Sanarwar da aka samu daga shafin Twitter a yammacin Juma’a ta tabbatar da shugaban Najeriya zai halarci zamansa na farko a taron ECOWAS.
Shugabanni da gwamnatocin kasashen da ke karkashin kungiyar ECOWAS na yammacin Afrika za su yi zama a birnin Bissau a ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng