Harin Masallacin Kaduna Ya Jefa Akalla Marayu da Mata 61 Cikin Garari, Inji Majiyar Kauye
- Rahoto ya bayyana halin matsi da tashin hankalin da ahalin wadanda aka kashe a masallacin Kaduna ke ciki a yanzu
- Majiya ta shaida cewa, akalla mutum 61 ne suka shiga garari ta dalilin kisan da ‘yan bindiga suka yiwa wasu mutum biyar
- Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fama da barnar masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yammacin Najeriya
Jihar Kaduna - Mutum hudu cikin wanda suka mutu a harin masallacin Kaduna, wanda ya yi sanadin rayuka kusan bakwai a daren Juma’a, sun bar marayu da zawarawa sama da 61, inji rahoton Daily Trust.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan masallata a lokacin da suke tsaka da sallah, inda suka yi ta kashe sy tare da raunata wasu dama a kazamin harin.
Wani manomi kuma dan kasuwa mai suna Ya’u Ibrahim mai ‘ya’ya 20 da mata biyu yana cikin wadanda aka kashe a harin.
An yi asarar masu rike da ahali
Sauran sun hada da kwamandan JTF da ake kyautata zaton shine makasudin abin da ‘yan bindigar suka zo kashewa, Malam Isiaka, wanda aka ce ya bar ‘ya’ya 17 da mata uku.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani mutumin kauye, Yunusa Nuhu ya mutu ya bar ‘ya’ya 14 da mata biyu, yayin da Malam Adamu da ke a Gidan Maidara ya bar ‘ya’ya 10.
Malam Dan Asabe Saya-saya, shugaban yankin da ya zanta da Daily Trust, ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa.
Matashi daya aka kashe a cikinsu
Ya kuma bayyana cewa, Mustapha Sale, dan shekara 25, shi kadai ne ba shi da mata a cikin wadanda aka hallaka.
A cewarsa:
“Kamar yadda kuka sani, dukkan mutane biyar da aka kashe a cikin masallacin ‘yan kauyen nan ne, amma sauran hudun an kashe su a kauyukan da ke kusa ne. Hakazalika, hudu daga cikin wadanda aka kashe a kauyenmu sun bar marayu da zawarawa 61.”
Ya ce iyalan wadanda abin ya shafa, musamman mata da kananan yara, na matukar bukatar agaji saboda rashin masu kula da su.
Yadda aka kai hari masallacin Kaduna
A tun farko, wasu da ake zaton yan bindiga ne sun farmaki masallata a wani masallaci a kauyen Saya-Saya da ke karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum bakwai.
An bindige mutum biyar a cikin masallacin, yayin da aka tsinci gawarwakin sauran mutanen biyu a wasu wurare daban-daban a cikin yankin, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, lamarin ya afku ne da misalin karfe 8:00 na dare lokacin da al'ummar kauyen ke sallar Isha'i a wani masallacin yankin.
Asali: Legit.ng