Kudi Ne Babbar Matsalar Najeriya, Davido Ya Hango Matsala, Ya Fadi Mafita Ga Rayuwa a Najeriya

Kudi Ne Babbar Matsalar Najeriya, Davido Ya Hango Matsala, Ya Fadi Mafita Ga Rayuwa a Najeriya

  • Mawakin Najeriya ya bayyana babban matsalar Najeriya, ya nemi shawarin ‘yan kasar kan yadda za a shawo kan abin da ke faruwa
  • Davido ya ce, kudi ne babban matsalar kasar nan, inda yace ko dai gwamnati ta hana amfani da kudi ne ma kawai kowa ya huta
  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da shan bakar wahala tun bayan janye tallafin man fetur da aka yi a watan Mayun wannan shekarar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kafar X - Fitaccen mawakin Afrobeat, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya ce kudi ne ummul haba'isin matsaloli a kasar nan.

Davido ya bayyana hakan ne a shafinsa na manhajar yanar gizo ta X a ranar Juma’a, 1 ga Satumba, kamar yadda Legit.ng Hausa ta gano.

A rubutun da ya yi ta yaduwa a yanar gizo, Davido ya tambayi mabiyansa ko ya dai ya nemi gwamnati ta hana amfani da kudi ne a kasar.

Kara karanta wannan

“Za a Iya Korarka Daga PDP” ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Kaca-Kaca da Wike

Kudi ne matsalar Najeriya, inji Davido
Davido ya ce kudi ne matsalar 'yan Najeriya | Hoto: @davido
Asali: Twitter

Kudi ne tushen matsaloli

A zancensa da ya yada, ya bayyana cewa, ya ma gano kudi ne babbar matsalar Najeriya a halin da ake ciki a yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Ko ya kamata su su hana amfani da kudi? Kudi ne ke haifar da matsaloli."

Sakon Davido ya haifar da musayar ra'ayoyi daban-daban daga mabiyansa. Wasu sun yarda da batunsa yayin da wasu suka saba da abin da ya fadi.

Halin da ake ciki a Najeriya

A halin yanzu, ‘yan Najeriya na ci gaba da dandana bakar wahala tun bayan da aka cire tallafin man fetur, inda kayayyaki suka yi tashin gwauron zabi.

Da yawa kan koka da cewa, harkokin kasuwanci da sana’o’in hannu sun yi cak a kasar duk dai a musabbabin cire tallafin.

A baya, akan siya litar man fetur a kasa da N300 a Najeriya, wanda a yanzu ake siyarsa sama da N600 a yankuna daban-daban na kasar.

Kara karanta wannan

'Wike Zai Kare a Gidan Yari', Wanda Aka Rusawa Gini Ya Sha Alwashin Shiga Kotu

An kone hoton Davido a Borno

A wani labarin, wasu matasa a Maiduguri babban birnin jihar Borno, sun fito kan titi don nuna fushinsu kan bidiyon da mawaki Davido ya wallafa a shafinsa na Twitter cikin 'yan kwanakin nan.

Mawaƙin ya sha suka biyo bayan dora wani bidiyo da bai yi wa Musulmin Najeriya dadi ba.

A cikin bidiyon, wanda wani mai suna Sultan ya wallafa a shafinsa na Twitter, matasan sun nemi Davido da ya fito ya bai wa Musulmin Najeriya hakuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.