Mutum 6 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Wani Hatsarin Mota a Jihar Osun

Mutum 6 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Wani Hatsarin Mota a Jihar Osun

  • Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ta tabbatar da aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Osun
  • Hatsarin motae wanda ya ritsa da motoci guda biyu ya yi sanadiyyar rasuwar mutum shida yayin da wasu suka tsira ba tare da raunika ba
  • Kwamandan hukumar FRSC na jihar ya yi kira ga direbobi da suka riƙa yin tuƙi mai tsafta domin kiyaye aukuwar haɗura

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Osun - Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Osun, ta bayyana cewa mutum shida sun rasa ransu a wani hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Imesi-Ile.

Kwamamdan hukumar, Mista Henry Benamesia, shi ne ya bayyana hakan ta hannun kakakin hukumar Mrs Agnes Ogungbemi, a birnin Osogbo, babban birnin jihar a ranar Lahadi, 3 ga watan Satumban 2023, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Dau Zafi Kan Kisan Masallata a Kaduna, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

Mutum shida sun rasu a wani hatsarin mota a Osun
Hoton wasu motoci da suka yi hatsari (ba inda lamarin ya auku ba) Hoto: PMnews.com
Asali: UGC

Yadda hatsarin ya auku

Benamesia ya bayyana cewa wasu motoci guda biyu sun yi taho mu gama a ranar Asabar da misalin ƙarfe 9:44 na dare a dalilin lalacewar birkin ɗaya daga cikinsu, wanda hakan ya janyo rasuwar mutum shida.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa wata mota (Red Daf) wacce ba ta da lamba, ta yi karo da wata babbar motar ɗaukan kaya mai koriyar kala a kusa da tsaunin Imesi-Ile a dalilin gudun da ya wuce ƙa'ida.

A kalamansa:

"Jami'an ƴan sanda sun kwashe gawar mutum biyar zuwa asibitin koyarwa na jami'ar jihar Osun (UNIOSUN) kafin zuwan tawagar jami'an hukumar FRSC."
"Gawar ƙarshe ta maƙale a ƙasan babbar motar inda mu ka samu samu mu ka ciro gawar daga baya."

A cewarsa, hatsarin ya ritsa da mutum 17, inda mutum 11 ba su samu raunika ba, sannan sai mutum shida da suka rasa ransu.

Kara karanta wannan

"Yadda Na Yi Kwamishina, Minista Ba Tare Da NYSC Satifiket Ba": Na Hannun Daman Buhari Ya Fasa Kwai

Kwamandan FRSC ya shawarci direbobi

Ya buƙaci direbobi da su riƙa yin tsaftataccen tuƙi domin kiyaye aukuwar haɗura a kan hanya.

Benamesia, ya kuma shawarci direbobi da su yi tuƙi cikin taka tsan-tsan da tabbatar da cewa motocinsu suna cikin yanayi mai kyau kafin su fara yin kowacce irin tafiya da su.

Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Mutum Biyu

A wani labarin kuma, wasu mutum biyu sun rasa ransu a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su a jihar Ondo.

Wasu mutum biyar kuma samu raunika a hatsarin motar wanda ya auku a kan titin Akure-Ondo a yammacin ranar Juma'a, 1 ga watan Satumban 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel