Za a Iya Binciken Buhari, Tsofaffin Shugabanni, a Radawa Najeriya Sabon Suna
- Wole Olanipekun ya na so Bola Ahmed Tinubu ya binciki magabatansa da su ka yi mulki a baya
- Gawurtaccen lauyan ya kawo shawarar a gano abin da ya jawo tabarbarewar abubuwa a Najeriya
- Daga cikin shawarar Olanipekun SAN shi ne a canzawa kasar nan suna, a daina kiran ta Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Babban lauya a Najeriya, Wole Olanipekun ya yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya binciki duka tsofaffin shugabannin da aka yi a kasar nan.
Vanguard ta ce Wole Olanipekun SAN ya na ganin binciken zai taimaka wajen gano abin da ya jawo Najeriya ta shiga irin halin da ta ke ciki a yau.
Lauyan ya ce ya kamata shugabannin kasar su amsa tambayoyi game da matsalar abubuwan more rayuwa, raunin tattalin arziki da rashin tsaro.
Lauyan Bola Tinubu da lauyan Atiku Abubakar
Rahoton ya ce Olanipekun SAN ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi biki domin taya Joe-Kyari Gadzama murnar zama babban lauya na kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar masanin shari’ar, ya kamata a fito da kudin da aka batar wajen farfado da tattalin arziki.
Jawabin Wale Olanipekun SAN
"Dole shugaban kasar ya yi tambaya, hakikanin muhimman tambayoyi, yadda mu ka shiga wannan yanayi mai ban tausayi; ta ya mu ka shiga babban kangi; menene abin da ya durkusa tattalin arziki; me ya faru da kasafin kudin da aka yi a baya da tiriliyoyin kudin da aka warewa gyaran hanyoyi, kiwon lafiya, tsaro, gyara abubuwan more rayuwa da gyara hukumomi da sauransu."
- Wale Olanipekun SAN
Jaridar Punch ta ce Olanipekun ya bukaci gwamnati ta ji dalilin da ya sa darajar Naira ya ke karyewa, ana canza kowace Dalar Amurka kan N900.
Dole gwamnati mai-ci ta binciki duka bayanai da kudin da aka kashe ko makamancin haka.
Ra’ayi na shi ne babu dalilin cin mutuncin kan mu ta hanyar cigaba da rike sunan Najeriya, munafukin sunan cin zarafin da mai dakin Lugard ta rada mana."
- Wale Olanipekun SAN
'Karyayyakin' Nyesom Wike
Dele Momodu ya ce Nyesom Wike ya lallabi Atiku Abubakar ya ba shi mukami a gwamnatinsa, ganin abin ya gagara, sai ya bi tafiyar Bola Tinubu.
Ana da labarin na kusa da Atikun ya karyata Wike a hirar da aka yi da shi, ya fallasa abubuwan da su ka faru a lokacin shirin zaben shugaban Najeriya.
Asali: Legit.ng