Aiki Ya Samu Yayin da Tinubu Ya Kira Dukkan Jakadun Najeriya Kan Su Dawo Kasar Nan Ba da Jimawa Ba

Aiki Ya Samu Yayin da Tinubu Ya Kira Dukkan Jakadun Najeriya Kan Su Dawo Kasar Nan Ba da Jimawa Ba

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkan jakadun Najeriya da su dawo gida nan wani lokaci a watan Oktoba
  • A tun farko, Tinubu ya kira daya daga jakadun Najeriya su dawo, sai kuma aka ce kiran ya shafi dukkan jakadun kasar
  • Aikin jakadun Najeriya dai ba komai bane face zama wakilan kasar a wasu kasashen waje, kuma shugaban kasa ke nada su

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a kirawo dukkan jakadun Najeriya da ke wakiltar Najeriya a kasashe daban-daban.

Yusuf Tuggar, Ministan Harkokin Waje, ya sanar da matakin ne sa'o'i 24 bayan da shugaban ya kira Sarafa Isola, babban kwamishinan Najeriya a Burtaniya, TheCable ta ruwaito.

A wata sanarwa da Alkasim Abdulkadir, mai ba Tuggar shawara kan harkokin yada labarai ya fitar ranar Asabar, ministan ya ce kiran da aka yi na Isola a ranar Juma’a ya shafi dukkan jakadun Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Sauya Wakilan Ondo da Cross River a Hukumar NDDC, Cikakken Bayani

Tinubu ya umarci dukkan jakadun Najeriya su dawo
Shugaban Najeriya ya umarci koran jakadun kasar | Hoto: Asiwjau Bola Ahmad Tinubu
Asali: Facebook

Kiran na nufin dakatar da dukkan jakadu

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 31 ga watan Agusta, ministan ya ce Tinubu ya kira Isola inda ya bukace shi da ya dawo Najeriya nan da ranar 31 ga watan Oktoba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A madadin Tinubu, Tuggar ya godewa babban kwamishinan mai gado bisa hidimarsa tare da yi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.

A cewar wasikar:

“Bayan bukatar aka bayyana wasikar kiran da aka yi wa jakadan Najeriya a Burtaniya, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya fayyace cewa ana kiran dukkan jakadun ne bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”

Meye aikin jakadun Najeriya?

Wani bangare na sanarwar da aka fitar ta bayyana kadan daga ayyukan da jakadun Najeriya ke yi a kasashen waje.

A cewar sanarwar:

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tsige Shugaban NASENI, Ya Nada ‘Dan Shekara 32 Ya Zama CEO

"Jakadu aikinsu wakilcin kasa ne bisa ga umarnin shugaban kasa kuma hakkinsa ne ya tura ko ya yi kiransu daga kowace kasa."

Ya zuwa yanzu dai Tinubu bai bayyana yaushe za a samar da wadanda za su wakilce su ba a nan gaba kadan ba, Channels Tv ta ruwaito.

An kori jakadun kasashe daga Nijar?

A wani labarin, hukumar sojin Nijar ta umarci jakadan Faransa ne kadai ya fice daga kasar, ba jakadun Jamus, Amurka ko Najeriya ba, in ji sanarwar da ta fitar, rahoton Anadolu Agency.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Juma'a, ma'aikatar ta yi watsi da rahotannin da ake yadawa da ke nuni da cewa an kori jakadun Jamus da Amurka da Najeriya, tare da bayyana cewa, Jakadan Faransa a Nijar ne kadai aka ayyana korarsa.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne gwamnatin mulkin sojan Nijar ta baiwa jakadan Faransa Sylvain Itte wa'adin sa'o'i 48 ya fice daga kasar, bisa zarginsa da kin amsa gayyatar da aka yi masa na ganawa da ministan harkokin wajen jamhuriyar.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Ware Biliyoyin Kudade Don Sake Gina Arewa, Ya Bayyana Dalili

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.