Khalil Suleiman Halilu: Wanene Mai Shekara 32 da Bola Tinubu Ya Nada Ya Rike NASENI

Khalil Suleiman Halilu: Wanene Mai Shekara 32 da Bola Tinubu Ya Nada Ya Rike NASENI

  • Khalil Suleiman Halilu ya zama shugaban hukumar NASENI, abin sha’awar shi ne shekararsa 32
  • Wannan Bawan Allah ya yi karatun firamare da sakandare a Kano kafin ya tafi jami’a a kasar Ingila
  • Khalil Halilu ya yi aikin kasuwanci da kamfanoni, kafin ya shiga harkar fasaha da ta kara fito da shi

Abuja - A yammacin Juma’ar nan aka samu labarin zaman Khalil Suleiman Halilu shugaban hukumar NASENI ta kasa.

A rahoton nan, mun tattaro bayanai game da wannan matashi da ake ta magana a kai ganin yadda ya samu babbar kujerar tarayya.

Shugaban NASENI
Shugaban NASENI, Khalil Suleiman Halilu Hoto: Babangida Yaya Jarmari
Asali: Facebook

1. Firamare da sakandare a Kano

Daily Trust ta ce a shekarar 1996 Khalil Suleiman Halilu ya fara karatun firamare a Rainbow Primary School a Kano, daga nan ya tafi makarantar St. Thomas Catholic domin yin sakandare a 2001, a karshe ya karasa a Prime College a 2006.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Sauya Wakilan Ondo da Cross River a Hukumar NDDC, Cikakken Bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Khalil Suleiman Halilu a jami’ar Ingila

Bayan nan ya tafi jami’ar Hertfordshire a kudancin Ingila, a nan ya samu digirin farko da na biyu a bangaren kasuwanci, ya kware a kasuwancin kasashen waje.

Legit.ng Hausa ta fahimci Khalil ya yi karatu a makarantu da cibiyoyin ilmi irinsu jami’ar John Hopkin, jami’ar Tenaris da cibiyar CFA duk a wajen Najeriya.

3. Aiki da kamfanoni kafin zuwa NASENI

Daga jami’a ya shiga aiki da kamfanin Archimode & Associates. Sannan a hankali ya zama Manaja a wani kamfani da ake kira Gongoni Company Limited.

Matashin ya yi shekaru uku a matsayin babban jami’in gudanarwa na kamfanin Scirrocco. Rahoton ya ce tun a shekara 23, ya fito da kan shi a kasuwanci.

A shekarar 2014 ya zama Darektan kamfanin Khash Strategic Services Ltd sannan ya yi aiki da Africa Infotech Consultancy a matsayin manajan gudanarwa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tsige Shugaban NASENI, Ya Nada ‘Dan Shekara 32 Ya Zama CEO

A shekarar 2017, Khalil ya sake rike babban matsayi a ZCET Global Meter Services Ltd

4. Khalil ya kama wani layin dabam

Bayan ya yi kwas a kan JAVA da DBA, sai ya saki layi daga kasuwanci zuwa harkar fasahar zamani.

A dalilin haka ya kafa kamfanin OyaOya Strategic Services Ltd da na ShapShap Logistics Ltd da ke saukakawa mutane sayen kaya a Afrika.

A 2018 kuma ya bude kamfanin Zabe da nufin sa ido a kan yadda ake gudamar da zabuka a Najeriya domin masu sa ido su san yadda ake ciki.

Kamar yadda hadimin shugaban kasa, Olusegun Dada ya sanar, shugaban na NASENI ne wanda ya kirkiro CANs da wani kamfani mai suna New AD.

Nadin mukamai a Kano

Ku na da labari Abba Kabir Yusuf ya cika alkawarin tafiya d amatasa, ya fitar da sunayen jerin sababbin SR da SSR da ma'aikatunsu a jihar Kano.

Abba Gida Gida ya yi haka ne domin ya jawo matasa cikin gwamnatinsu ta Jam’iyyar NNPP watanni uku bayan ya gaji Dr. Abullahi Umar Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng