Shugaba Tinubu Ba Ya Tunanin Nada Ni Gwamnan CBN, In Ji Elumelu
- Tony Elumelu ya musanta rahoton cewa shugaban ƙasa Tinubu na shirin naɗa shi a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN)
- Shugaban kamfanin Heirs Holdings kuma tsohon shugaban bankin UBA ya ce labarin ƙanzon kurege ne, bai da tushe
- A 'yan kwanaki kalilan da suka shige, Elumelu ya ziyarci shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja
FCT Abuja - Tony Elumelu, Shugaban Kamfanin Heirs Holdings, ya musanta rahotannin da ke cewa da yiwuwar shi zai zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) na gaba.
A wani sako da ya wallafa a Shafin X, wani Imran Muhammad ya ruwaito wata majiya na cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na tunanin naɗa Elumelu ya jagoranci babban bankin.
"A cewar wata majiya, Shugaba Tinubu na tunanin nada Tony O. Elumelu a matsayin gwamnan CBN," in ji Imran.
Menene gaskiyar wannan batu?
Sai dai da yake maida martani kan wannan ikirari, Elumelu ya bayyana cewa ko kaɗan labarin ba gaskiya bane, inda ya wallafa cewa, "A'a dan Allah, wannan labarin ƙarya ne."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Elumelu babban ma’aikacin banki ne da ya taka matakin nasara, wanda ya yi aiki a matsayin shugaban bankin United Bank for Africa (UBA), daya daga cikin manyan bankunan kasuwanci a Najeriya, mai rassa a fadin duniya.
Haka zalika a baya bayan nan, shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya karɓi bakuncin Elumelu a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Mista Elumelu yana ɗaya daga cikin baki masu jawabi a wurin taron kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da aka kammala, wanda shugaba Tinubu ya ayyana budewa.
Har yanzu ba bu gwamna a CBN
Wannan jita-jita na zuwa ne bayan shugaban ƙasa ya dakatar da Godwin Emefiele daga matsayin gwamnan babban bankin Najeriya.
Jim kaɗan bayan dakatar da shi, jami'an tsaron farin kaya DSS suka damƙe shi bisa tuhume-tuhume da dama da suka haɗa da mallakar haramtattun makamai da sauransu.
Tinubu Ya Tsige Shugaban NASENI, Ya Nada ‘Dan Shekara 32 Ya Zama CEO
A wani rahoton na daban, Bola Ahmed Tinubu ya sallami Dr. Bashir Gwandu daga kujerar da ya ke kai ta babban shugaban hukumar nan ta NASENI.
Tinubu ya dauko Khalil Suleiman Halilu, ɗan kimanin shekara 32 a duniya, ya naɗa shi a matsayin sabon shugaban hukumar kasar.
Asali: Legit.ng