"Mun Yi Asara Sakamakon Raguwar Amfani Da Man Fetur A Najeriya Da Kaso 30", Shugaban NNPC, Mele Kyari

"Mun Yi Asara Sakamakon Raguwar Amfani Da Man Fetur A Najeriya Da Kaso 30", Shugaban NNPC, Mele Kyari

  • Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ya bayyana cewa an samu raguwar amfani da man fetur a kasar da kaso 30
  • Kyari ya ce wannan bai rasa nasaba da cire tallafin mai da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi a watan Mayu da ta gabata
  • Kyari ya ce an samu raguwar amfani da mai din daga lita miliyan 66.7 kafin cire tallafi zuwa lita miliyan 46 bayan cire tallafi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kamfanin mai na NNPC ya nuna damuwarsa kan yadda 'yan Najeriya su ka rage siyan mai tun bayan cire tallafin da Shugaba Tinubu ya yi.

Kamfanin ya ce an samu raguwar amfani da mai din da kaso 30 cikin dari a kasar idan aka kwatanta da watannin baya.

NNPC ya bayyana asarar da ya yi saboda raguwar amfani da mai a Najeriya
Kamfanin NNPC Ya Yi Martani Kan Raguwar Shan Mai A Najeriya. Hoto: Mele Kyari, NNPC.
Asali: UGC

Meye NNPC ya ce game da man?

Kara karanta wannan

'Wike Zai Kare a Gidan Yari', Wanda Aka Rusawa Gini Ya Sha Alwashin Shiga Kotu

Shugaban kamfanin, Malam Mele Kyari shi ya bayyana haka a yau Juma'a 1 ga watan Satumba a Abuja yayin ganawa da manema labarai, PM News ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ganawar tare da Kyari akwai ministan kudade da tsara tattalin arziki, Wale Edun a Abuja.

Kyari ya ce an samu raguwar shan mai din daga lita miliyan 66.7 kafin cire tallafi zuwa lita 46 bayan cire tallafi.

Kyari ya kara da cewa hakan ya nuna an samu raguwar kaso 30 daga cikin dari na amfani da mai din a kasar.

NNPC ya bayyana dalilin raguwar siyan mai din

Ya ce zuwa ranar Wednesday 30 ga watan Agusta, an samu karuwar fitar da man fetur zuwa lita miliyan 1.6.

Wannan na zuwa ne bayan samun kasa da lita miliyan daya a watannin da su ka wuce, cewar jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

‘Abun da Tinubu ya Fada Mani Bayan Nada Ni Ministan Abuja’, Wike Ya Bayyana

NNPC ya bayyana cewa wannan raguwar bai rasa nasaba da cire tallafin mai da aka yi a kasar.

Najeriya Ta Yi Asarar Dala Biliyan 46 Na Danyen Mai Saboda Sata

A wani labarin, Kamfanin mai na NNPC ya ce ya yi asarar fiye da Dala biliyan 46 na gangan danyen mai miliyan 612 a cikin shekaru 10.

NNPC ya ce yawan satar mai da ake a kasar ya wuce hankali wanda hakan ke jawo wa kamfanin da Najeriya asara ta makudan kudade.

Wannan na zuwa ne bayan kamfanin ya afka asarar biliyoyin Daloli sakamakon satar danyen mai musamman a jihohin da su ke da arzikin mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.