Wasu Matasa Sun Yi Garkuwa Da Matan 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara

Wasu Matasa Sun Yi Garkuwa Da Matan 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara

  • Wasu mazauna yankin Birnin Magaji da ke jihar Zamfara sun yi garkuwa da wasu matan 'yan bindiga a yankin
  • Wannan na zuwa ne bayan 'yan bindigan sun sace wasu mutane bakwai su na tsaka da aiki a cikin gonarsu
  • Matasan da su ka kama matan 'yan bindigan sun ce ba za su sake matan ba har sai an sako musu 'yan uwansu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - Yayin da 'yan bindiga su ka addabi yankunan jihar Zamfara, mutane sun gano salon ramawa.

Wasu mutane sun yi garkuwa da matan 'yan bindiga a yankin Birnin Magaji da ke jihar Zamfara.

Matasa sun sace wasu matan 'yan bindiga a jihar Zamfara
Matasa Sun Sace Matan 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara. Hoto: @DaudaLawalD/X.
Asali: Facebook

Me yasa matasan su ka sace matan 'yan bindigan?

Wannan na zuwa ne ganin yadda 'yan bindigan su ka hana jama'a sakat da sace-sace da kuma kashe-kashe.

Kara karanta wannan

“Na Gaji Da Su”: Wani Dan Shekaru 55 Ya Saki Matansa 3 a Rana Daya, Ya Fallasa Zunubansu a Bidiyo

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahotanni sun tabbatar cewa matasan sun yi hakan ne don martani game da satan wasu mutane bakwai da 'yan bindigan su ka yi a gona.

Matasan sun kuma yi wa 'yan bindigar barazana kan kama 'yan yankin nasu da su ka yi.

Sun sha alwashin cewa ba za su sake matan ba har sai su ma 'yan bindigan sun sake musu mazajen da su ka sace musu.

Aminiya ta tattaro cewa wani mazaunin yankin ya bayyana yadda sace matan 'yan bindigan ya faru.

Meye mutane ke cewa kan 'yan bindigan?

Ya ce:

"Mu na cikin jimamin sace 'yan uwanmu ne kawai sai muka hango matan 'yan bindigan sun zo wucewa ta inda mu ke."

Ya ce daga nan ne mutane su ka sace su tare da cewa ba za su sake su ba har sai an dawo musu da 'yan uwansu.

Kara karanta wannan

Dan Daudu Bobrisky Ya Goyi Bayan Kama 'Yan Luwadi 100 Da Aka Yi a Jihar Delta, Ya Ba Da Dalili

Ya kara da cewa 'yan bindigan sun yi waya da matan inda su ka roki mazajen nasu da su yi kokari a sake su don su na cikin mawuyacin hali.

Wata majiyar BBC ta ce mutanen su na cikin aiki a gona sai 'yan bindiga fiye da goma su ka zagaye su da makamai tare da tafiya da su.

Daga cikin mutanen da aka sacen daya ya samu damar kubucewa yayin da maza hudu da mata ke hannun 'yan bindigan.

Sojin Sama Sun Yi Ajalin Aliero Da Dankarami A Zamfara

A wani labarin, rundunar sojin sama sun yi ajalin shugabannin 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Wadanda aka kashen sun hada da Ado Aliero da kuma Dankarami da su ka addabi yankunan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.