Ogun: Fasto Ya Cinnawa Wata Budurwa Wuta Lokacin Yi Mata Addu'a
- Faston cocin Cherubim and Seraphim church, Taiwo Odebiyi, ya shiga hannun jami'an ƴan sandan jihar Ogun
- Fasto Odebiyi ya bankawa wata budurwa mai suna Sukura Owodunni mai shekara 21 wuta a lokacin da ya ke yi mata addu'a a harabar cocin
- Faston dai ya sanya wa budurwar wani turare ne a jikinta sannan ya kunna kyandir a lokacin da ya ke mata addu'ar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Sagamu, jihar Ogun - Fasto Taiwo Odebiyi na Cherubim and Seraphim Church, Maberu Parish wacce ke a Offin a yankin Sagamu na jihar Ogun, ya shiga hannun jami'an ƴan sanda bisa cinnawa wata budurwa wuta.
Faston dai ya cinnawa budurwar mai suna Sukura Owodunni, mai shekara 21 a duniya wuta ne lokacin da ya ke yi mata addu'a ta musamman.
Kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto, lamarin ya auku ne a ranar 17 ga watan Agustan 2023.
Yadda fasto ya ƙona budurwa wajen addu'a
An tattaro cewa faston ya buƙaci Sukura ta siyo turaren 'Amazing Grace', ƙwai da kyandir. Lokacin da faston ya ke yi mata addu'a sai ya ƙwarara mata turaren a jikinta sannan ya kunna kyandir ɗin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Nan da nan wuta ta kama a jikin budurwar wacce ta haddasa mata samun mummunar ƙuna a ƙirji, kafaɗa da ƙafafu, rahoton Chronicle ya tabbatar.
A cewar wani shaidar ganau ba jiyau ba, DPO na ƴan sandan Adigbe, CSP Abdulfattah Ogunsanya, da jami'ansa sun dira cocin inda suka yi caraf da faston.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ogun, SP Omolola Odutola, wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta bayyana cewa:
"An ƙyale budurwar tana ɗawainiyar na magani da kanta bayan aukuwar lamarin."
"Jami'an mu sun cafke wanda ake zargin. Za a tura lamarin zuwa sashen binciken laifuffuka bayan an kammala binciken farko."
Matashi Ya Halaka Mahaifinsa
A wani labarin kuma, wani matashi ya salwantar da rayuwar mahaifinsa mai shekara 100 a duniya bayan sun samu saɓani a kan kuɗi.
Matashin dai ya sanya adda ya sari mahaifinsa wacce ta yi sanadiyyar mutuwarsa bayan sun samu saɓani a kan N70,000. Matashin ya ce ya halaka shi ne bayan ya ƙi dawo masa da kuɗinsa da ya ba shi ajiya.
Asali: Legit.ng