Kungiyar Arewa Ta Zargi Tinubu Da Mayar Da Gwamnati Ta Yarbawa Zalla, Ta Yi Nemi A Gyara
- Kungiyar Raya Arewacin Najeriya, AEF ta soki tsarin Tinubu na nuna wariya a mukaman gwamnati
- Kungiyar ta ce a hankali Tinubu ya na sauya 'yan Arewa da maye gurbinsu da Yarbawa a wasu manyan hukumomi
- Ta bayyana rashin jin dadinta ganin yadda shugaban ya samu kuri'u masu tarin yawa a yankin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Wata kungiya a Arewacin Najeriya, Arewa Economic Forum (AEF) ta soki tsarin yadda Shugaba Bola Tinubu ke nade-naden mukamai a gwamnatinsa.
Kungiyar ta ce Tinubu ya fifita bangaren Yarbawa da kuma jihar Legas inda kungiyar inda ta ce hakan ya zama ‘Yarbawanantar’ da gwamnati.
Meye Arewa ke zargin Tinubu a kai?
Shugaban kungiyar, Ibrahim Shehu Dandakata shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a jiya Laraba 30 ga watan Agusta a Abuja, cewar Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce mafi yawan masu rike da manyan mukamai wadanda 'yan Arewa ne, Tinubu ya sauya su da Yarbawa wadanda mafi yawansu daga jihar Legas.
Wane shawara Arewa ta bai wa Tinubu?
Yayin da kungiyar ke nuna rashin jin dadinta kan yadda ake nuna wariya, Dandakata ya shawarci Shugaba Tinubu da ya yi abin da ya dace tun kafin lokaci ya kure.
Ya ce yankin Arewa ta ba da gudumawar wurin hawan gwamnatin Tinubu, amma kuma ko kadan ba ta jin dadin yadda ake raba mukaman a gwamnatin na Shugaba Tinubu.
Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda Tinubu ya sauya manyan shugabannin hukumomin gwamnati da wadanda ‘yan Arewa ne a hankali ake maye gurbinsu da Yarbawa.
Ya karada cewa akwai hasashen za a ci gaba da maye gurbin 'yan Arewa a nan gaba ganin yadda aka nuna wariya tun farko, Tribune ta tattaro.
Tinubu: Sanwo-Olu Na Legas Ya Roki Jama'a Su Kara Hakuri
A wani labarin, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya roki 'yan Najeriya da cewa su kara hakuri da sabbin tsare-tsaren Shugaba Tinubu.
Sanwo-Olu ya bayyana haka ne a jiya Laraba 30 ga watan Agusta a Abuja yayin ganawa da uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu.
Asali: Legit.ng