Hadarin Kwale-kwale Ya Yi Sanadiyyar Batan Mutane 6 a Jihar Neja
- Mutane 6 ne aka tabbatar da ɓatansu a wani haɗarin kwale-kwale a Neja
- An bayyana cewa mutanen suna kan hanyarsu ta zuwa jihar Kebbi da ke makwabtaka da su ne
- An bayyana cewa mummunan lamarin ya kuma rutsa da mata da kuma kananan yara
Neja - Mutane aƙalla 6 ne aka tabbatar da ɓatansu a wani haɗarin kwale-kwale da ya rutsa da su a Kogin Zamare da ke ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja.
Mummunan lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin, 28 ga watan Agustan da muke ciki kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yadda mutane 6 suka bata a haɗarin kwale-kwale
An bayyana cewa lamarin ya rutsa ne da mutanen da mafi akasarinsu manoma ne da ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Kebbi da ke makwabtaka da Neja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mazauna yankin sun shaidawa manema labarai cewa masu ceto sun yi nasarar gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda suka ɓata, yayin da ake ci gaba da neman sauran.
An bayyana cewa kwale-kwalen yana ɗauke da fasinja aƙalla 20 ne a yayin da injinsa ya mutu a tsakiyar kogin, wanda hakan ne ya janyo haɗarin na sa.
Hadarin ya rutsa da mata da ƙananan yara
An kuma bayyana cewa daga cikin waɗanda haɗarin kwale-kwalen ya rutsa da su akwai mata da kuma ƙananan yara.
Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Garba Salihu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce har yanzu hukumar ba ta samu cikakken bayani ba.
Ana yawaitar samun haɗurran kwale-kwale a sassa daban-daban na Najeriya, inda ko a kwanakin baya sai da Legit.ng ta yi rahoto kan wani haɗarin da ya rutsa da mutane 8 a jihar Zamfara
Hadarin jirgin ruwa ya rutsa da mutane 100 a Kwara
Legit.ng a kwanakin baya ta yi wani rahoto kan wani mummunan haɗarin jirgin ruwa da ya rutsa da mutane 100 a wani ƙauye na jihar Kwara.
Wannan lamarin ya faru ne a yayin da mutanen suke kan hanyarsu ta dawowa daga wani ɗaurin aure da aka yi a jihar Neja.
An bayyana cewa mutane da dama ne suka rasa ransu a mummunan haɗarin jirgin da ya faru a lokacin.
Asali: Legit.ng