Mutane 15 sun mutu a mummunan hatsarin kwale-kwale a jahar Neja

Mutane 15 sun mutu a mummunan hatsarin kwale-kwale a jahar Neja

Akalla mutane 15 ne suka rasa ransu a sanadiyyar hadarin kwale kwale daya faru a cikin karamar hukumar Borgu ta jahar Neja, yayin da wasu da dama suka samu munanan rauni, inji rahoton jaridar Guardian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hadarin ya rutsa da matafiya ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwar Wara dake kan iyaka da karamar hukumar Ngaski na jahar Kebbi, inda suka nufi Sabo Yumu da tsakar daren Laraba, 31 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Gwamnoni 5 na Arewa maso yamma zasu gana da juna game da matsalar tsaro a Katsina

Wannan hadari ya auku ne sanadiyyar rashin yanayi mai kyau wanda yasa matukin kwale kwalen ya ci karo da wani katon bishiya dake cikin tafkin Malale. “An gano gawarwaki guda 15, kuma an binnesu, yayin da aka ceto mutane 2, amma har yanzu akwai wadanda ba’a gano inda suke ba.

“Kwale kwalen babba ne, domin yana cin fasinjoji 50, bugu da kari ranar cin kasuwa ne, akwai yiwuwar an cika fasinjoji da kaya a cikin jirgin” Inji shi.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Neja, NSEMA, Alhaji Ibrahim Inga ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace akalla mutane 15 sun rasa ransu, amma ana cigaba da neman sauran mutanen da ba’a gansu ba.

Inga ya ce gwamnatin jahar na duba yiwuwar sanya idanu tare da dokoki ga matuka kawale kwale tare da raba rigar ruwa ga matafiya don magance irin wannan matsala a gaba, musamman duba da yadda ake yawan samun irin wannan haddura a jahar.

Tafkin Malale ya yi kaurin suna wajen ire iren hadduran nan musamman a lokacin damina, inda ko a shekarar 2017 sai da irin wannan hadari ya kashe mutane 8, mata da kananan yara yayin da suke kan hanyar zuwa Malale daga kasuwar Wara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel