Sojojin Najeriya Sun Fara Daukar Mataki Bayan Juyin Mulkin Da Aka Yi a Kasar Gabon
- Kwamandan runduna ta 81 a gidan sojojin kasa ya nemi dakarun Najeriya da yin cikakkiyar biyayya
- Janar Mohammed Takuti Usman ya fadawa jami’ansa cewa dole ne soja ya yi wa shugabanninsa da’a
- Ganin ana ta juyin mulki a Afrika, GOC ya ce duk sojan da bai da shirin yin biyayya, ya ajiye khaki
Ogun - Babban kwamandan da yake rike da dakarun sashe na 81 na sojojin Najeriya, Mohammed Takuti Usman ya gargadi jami’ansa a jihar Enugu.
Manjo Janar Mohammed Takuti Usman ya bukaci sojojin da su ke aiki da shi su zama masu biyayya ga Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabanni.
Daily Trust ta rahoto babban jami’in ya na cewa ya zama dole sojoji su zama masu da’a a kullum.
Sojoji sun yi juyin mulki a Gabon
Janar Mohammed Takuti Usman ya yi wannan kira ne da yake magana da rundunar sojojin yaki na reshen Alamala a babban birnin Ogun; Abeokuta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda GOC din ya shaidawa sojojin kasan, dole sai sun nuna sanin aiki da kuma cikakkiyar biya ga mai girma shugaban kasa da sauran jagorori.
Ganin an yi juyin mulki a kasar Gabon ne Mohammed Takuti Usman ya yi wannan kira saboda gudun sojojin Najeriya su fara kwadayin kifar da mulki.
Shugaban dakarun na Alamala, Birgediya Janar Mohammed Tajudeen Aminu ya na gefen Manjo Janar Mohammed Takuti Usman da yake yin jawabin.
Soji ya cire tunanin juyin mulki
An rahoto sojan ya na cewa shakka babu akwai kalubalen da ake fama da su, amma abin ruwan dare ne kuma duk wanda ba zai yi da’a ba, ya bar aikinsa.
“Yayin da mu ke duba kalubalen da yadda za mu magance su, tole ne ku zama sojoji masu da’a, dole ku zama sojoji masu biyayya.
Idan na ce biyayya, ina nufin biyayyarku ta fara da shugaban dakarun Najeriya, wanda shi ne shugaban kasa a wannan tsani.
Sai biyayya ga shugaban hafsun tsaro, shugaban hafsun sojojin kasa, zuwa shugaban rundunarku.
Dole ku zama masu biyayya. Babu wurin zaman sojojin da ba su biyayya ga shugabanni. Idan ba za ku da'a ba, ku tafi neman wani aiki."
- Manjo Janar Mohammed Takuti Usman
Bugaje: "Ba za mu yaki Nijar ba"
Idan yaki ya barke da Nijar, kun samu labari Dr. Usman Bugaje ya ce za a iya samun tasgaro a shari’ar zaben shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi ta mulki.
Tsohon ‘dan majalisar tarayyar ya na ganin idan Najeriya za ta yaki Nijar saboda dawo da Mohammed Bazoum, ba za su shiga cikin dakarun kasar nan ba.
Asali: Legit.ng