Ku Fuskanci Aikin da Ke Gabanku, Kungiyar Kasashen AU Ta Yi Gargadi Mai Zafi Ga Jagororin Juyin Mulkin Gabon
- Rahoton da ke iso mu ya bayyana yadda kungiyar AU ta yi Allah wadai da yadda aka yi juyin a jamhuriyar Gabon kwanan nan
- An sanar da kwace mulki a hannun shugaban farar hula na Gabon bayan kaddamar da zaben da aka ce akwai murdiya
- Har yanzu ba a kammala warware matsalar juyin mulkin Nijar da sojin jamhuriyar suka yi a kwanakin baya da suka gabata
Addis Ababa, Habasha - A ranar Laraba, shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat, ya gargadi sojojin kasar Gabon da jami'an tsaro da su yi aikin da ya rataya a wuyansu na jamhuriyar.
Hakan dai na zuwa ne yayin da ya kuma yi kakkausar suka ga abin da ya bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki a Gabon, Vanguard ta ruwaito.
Jami'an 'yan tawaye a kasar ta tsakiyar Afrika mai arzikin man fetur, sun sanar a safiyar Laraba cewa, sun kwace mulki, sakamakon kitmurmura a zabukan da aka takaddamar a kasar.
Dalilin juyin mulki a Gabon
A zaben da aka gudanar, an ayyana shugaba Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya lashe zaben, lamarin da ya jawo cece-kuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba, a tarihin jamhuriyar Gabon, Bongo ya da ahalinsa ne ke mulkar kasar na tsawon shekaru 55.
Duk da haka, ana yiwa kallon mulkin da suke yi a matsayin dimokradiyya duk da kuwa ya fi kama da mulkin gado na ‘yan kama karya.
Bayanan Kungiyar AU
A cewar sanarwar da AU ta buga a shafinta:
"(Faki) yana bibiyar halin da ake ciki a jamhuriyar Gabon tare da yin Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar a matsayin hanyar warware rikicin da take ciki a yanzu bayan zaben shugaban kasa.
Fargabar Juyin Mulki: Rwanda, Kamaru Sun Dauki Tsauraran Matakai Kan Rundunar Tsaronsu, Sun Bayyana Matakan
“Ya kuma yi kira ga sojojin jamhuriyar da jami’an tsaro da su dukufa fa aikin jamhuriyarsu don tabbatar da kare mutuncin shugaban jamhuriyar, iyalansa da na gwamnatinsa.”
Hakazalika, ya bayyana abin da ya faru a Gabon a matsayin ketare haddi da kuma shiga alfarmar shugaban kasar.
Yunkurin ECOWAS game da rikicin Nijar
A bangare guda, an tattauna game da yanayin da ya zo na juyin mulkin Nijar da ya faru a kwanakin bayan nan a kasar.
Dr. Usman Bugaje ne ya bayyana bayanai ma su muhimmanci game da matsayar ECOWAS game da juyin mulkin na Nijar.
Idan baku manta ba, ECOWAS na bayyana fushi tare da nuna alamar daukar mataki kan abin da ya faru a jamhuriyar Nijar.
Asali: Legit.ng