Abba Gida Gida Ya Yi Alkawarin Sauya Tunani Da Kuma Kulawa Da Tubabbun ’Yan Daba 100 Na Kano
- Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin gyara tunani da kuma samar wa tubabbun ‘yan daba sana’o’i
- Abba Kabir ya bayyana haka ne yayin da ya ke karbar tubabbun ‘yan daban guda 100 da kwamishinan ‘yan sanda ya mika masa
- Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban daraktan hadimai na gidan gwamnati, AVM Ibrahim Umar ya godewa ‘yan sandan bisa kokarinsu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi alkawarin inganta rayuwar tubabbaun ‘yan daba dari da aka mika masa.
Abba Gida Gida na magana ne bayan kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Mohammed Gumel ya mika masa su inda ya sha alwashin gyara musu tarbiya don gobe.

Source: Facebook
Meye Abba Kabir ya ce kan tubabbun a Kano?
Gumel ya gabatar da tubabbun ‘yan daban ne a filin wasa na Sani Abacha yayin karkare wasan kwallon kafa ta sada zumunta a Kano.

Kara karanta wannan
Gwamnan Jihar Arewa Ya Ba Da Umarnin Rufe Makaranta Saboda Mummunan Laifin Da Aka Aikata a Cikinta
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abba Kabir wanda ya samu wakilcin babban daraktan hadimai na musamman daga gidan gwamnati, AVM Ibrahim Umar ya yabawa Gumel kan wannan kokari na shi, PM News ta tattaro.
A cewarsa:
“Wadannan tubabbun ‘yan daba da kwamishina ya mika mana, gwamnatin jihar ta karbe su hannu bibbiyu.
“Kuma za mu dauki bayanansu tare da ba su ayyukan da za su yi wanda gwamnatin jihar za ta dauki nauyi.”
Abba Kabir ya sha alwashin kawo karshen tsaro a Kano
Gwamnan ya kara da cewa a lokacin rantsuwar karbar mulki ya yi alkawarin yaki da masu aikata laifuka da dama inda ya ce rashin tsaro ya yi katutu, cewar Tribune.
Ya kuma yi alkawarin gyaran wutar kan tituna wanda ya ke matukar taimakawa wurin aikata laifuka da dare.
A martaninshi, Kwamishina Gumel ya bukaci al’umma da kada su nuna wani wariya ga tubabbun ‘yan daban inda ya ce sun yi alkawarin ba za su sake aikta laifi ba.
Kasurgumin Dan Daba Da Ake Nema Ya Mika Wuya A Kano
A wani labarin, kasurgumin dan daban nan da ake nema ruwa a jallo, Chile mai Doki ya mika wuya ga jami'an 'yan sanda a jihar Kano.
Idan ba a mantaba kwamishinan 'yan sanda a jihar, Moohammed Gumel ya saka kyautar Naira dubu 300 ga dukkan wanda ya kawo wasu 'yan daba uku da ake nema.
Daga bisani Chile mai Doki wanda ya ke daga cikinsu ya mika wuya tare alkawarin sauya halayensa.
Asali: Legit.ng
