Gwamna Bala Na Bauchi Ya Bada Umurnin Rufe Makaranta Kan Kisan Wani Yaro
- Gwamna Bala na Bauchi ya ba da umarnin rufe wata makaranta har sai baba ta gani
- Gwamnan ya ɗauki matakin ne biyo bayan gawar wani yaro da aka tsinta da aka cire wasu sassa na jikinsa
- Ya umarci jami'an 'yan sandan jihar da su baza komarsu wajen zaƙulo waɗanda suka aikata mummunan aikin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya ba da umarnin rufe makarantar da aka tsinci gawar wani yaro mai suna Mohammed Abidin Musa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da ya je yi wa iyayen yaron da aka kashe jaje da kuma ta'aziyya kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.
Gwamnan Bala ya damu kan kisan yaro a makaranta
Gwamna Bala ya nuna damuwarsa matuƙa kan mummunan kisan da aka yi wa yaron wanda bai ji ba bai gani ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana kisan a matsayin mummunan laifi abin ƙi, inda ya kuma ba da tabbacin cewa jami'an 'yan sandan jihar na iya bakin ƙoƙarinsu wajen gano wadanda ke da hannu a ciki.
Ya kuma yi addu'ar Allah ya gafartawa yaron, sannan kuma ya yi kira ga iyaye da su ƙara sanya idanu a kan yaransu da kewayensu.
Yadda aka tsinci gawar yaron a makaranta
A rahoton da jaridar The Nation ta wallafa, an tsinci gawar Mohammed Abidin ne a cikin mummunan yanayi na cire wasu sassa na jikinsa da aka yi.
Gwamna Bala ya koka kan yadda ake ƙara samun yawaitar ayyuka na ta'addanci a jihar Bauchi, wacce ta kasance hanyar shiga jihohi aƙalla bakwai da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Daga ƙarshe gwamnan ya ba da tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar al'ummar jihar baki ɗaya.
Gwamnatin jihar Bauchi ta kulle makarantu 5 saboda cutar mashaƙo
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan rufe wasu makarantu guda biyar da gwamnatin jihar Bauchi ta yi sakamakon rahoton ɓullar cutar mashaƙo da aka yi a cikinsu.
Gwamnatin ta kuma ba da tabbacin cewa za ta rufe duk wata makaranta da aka samu ɓullar cutar ba tare da ɓata lokaci ba.
Asali: Legit.ng