Kungiyar Musulunci Ta Aike Da Sako Mai Muhimmanci Ga Sojojin Najeriya Kan Juyin Mulkin Gabon
- MURIC ta yi martani bayan hambarar da gwamnatin farar hula da sojoji suka yi a kasar Gabon
- Kungiyar ta kare hakkin Musulmi ta gargadi sojojin Najeriya a kan koyi da takwarorinsu na gabon
- A cewarta duk wani sojan Najeriya da ya yi kokarin juyin mulki zai yi ne saboda dalilai na son zuciya, cewa siyasar kasar ya sha bamban da na Gabon
Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta shawarci rundunar sojojin Najeriya da kada ta yi koyi da sojojin Gabon da suka hambarar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo a ranar Laraba.
Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayar da shawarar a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, Daily Trust ta rahoto.
Siyasar Najeriya ta sha bamban da na Gabon, MURIC
Akintola ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Yayin da muke fushi da tsarin da iyalin Bongo a Gabon da wasu kasashen Afrika ke bi, muna Allah wadai da wannan juyin mulkin sojojin. MURIC ta shawarci sojojin Najeriya da su ci gaba da cire bakinsu daga harkokin siyasa sannan su guji kwadayin son koyi da sojojin Gabon ta hanyar yin juyin mulki a Najeriya.
“Duk wani sojan Najeriya da ya yi tunanin juyin mulki a halin yanzu yana yin haka ne saboda dalilai na son zuciya. Ya kamata a lura cewa siyasar Najeriya ta sha bamban da na Gabon inda daular Bongo ta shafe fiye da shekaru 50 akan karagar mulki.
"Za a fassara juyin mulkin sojoji kan tikitin Musulmi da Musulmi da ake kai yanzu a matsayin hari kai tsaye ga Musulmai a kasar idan aka yi la'akari da takkadamar da ke kewaye da tikitin Musulmi da Musulmin.
"Duk wani juyin mulki yanzu a Najeriya zai shafi addini ne. Najeriya ba ta farfado daga juyin mulkin bangare guda na kin jinin arewa da sojojin Inyamurai suka yi a ranar 15 ga watan Janairun 1966 ba da kuma na daukar fansa da sojojin arewa suka yi a Yulin 1966 ba."
Yan Najeriya na alfahari da rundunar sojin kasar, MURIC
Ya ce rundunar sojojin Najeriya sun samu horo mai kyau da kwarewa a kan aiki kuma yan Najeriya na alfahari da su.
Shugaban MURIC din ya kuma bayyana cewa hannun rundunar sojin Najeriya cike yake da aiki kama daga yaki da Boko Haram, masu tayar da kayar baya da sauran masu kawo barazana ga tsaro, don haka ba za ta iya kara siyasa a kalubalanta ba.
Yan farar hula a Gabon sun yi murnar juyin mulki da sojoji suka yi
A wani labarin, mun ji a baya cewa masu goyon bayan kwace mulki da sojoji suka yi a kasar Gabon da dama sun yi tururuwar fitowa kan titinunan unguwanninsu.
Hotunan da Legit.ng ta gano sun nuna al'ummar garo suna jinjinawa dakarun rundunar tsaro a yankin Plein Ciel da ke Libreville, babban birnin kasar Gabon.
Asali: Legit.ng