Najeriya Ta Yi Nasarar Biyan Bashin Dala Biliyan 1.17 Ga Kasar Sin Da Bankin Duniya

Najeriya Ta Yi Nasarar Biyan Bashin Dala Biliyan 1.17 Ga Kasar Sin Da Bankin Duniya

  • Rahoton Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa Najeriya ta biya bashin Dala biliyan 1.17 a farkon 2023
  • A cikin dukkan watannin da aka biya bashin, watan Yuni ya fi muni ganin yadda ya kai Dala miliyan 543
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban kasa, Bola Tinubu ya sha alwashin kawo karshen basukan da kasar ke ciyowa

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta biya bashin Dala biliyan 1.17 a farkon wannan shekarar ta 2023.

Babban Bankin Najeriya, CBN shi ya tabbatar da haka a cikin wani rahoton da ya fitar.

Najeriya ta biya bashin Dala biliyan 1.17 a farkon watanni shida na 2023
Jimillar Basukan Da Najeriya Ta Biya A Farkon 2023 Ya Kai Dala Biliyan 1.17. Hoto: CBN, FG.
Asali: UGC

Meye CBN ta ce kan bashin Najeriya?

Legit.ng ta tattaro cewa, Najeriya na kashe kimanin kaso 85 na kudaden shuganta wurin biyan basuka a watan Faburairu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

‘Abun da Tinubu ya Fada Mani Bayan Nada Ni Ministan Abuja’, Wike Ya Bayyana

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin kawar da wannan al'ada ta kashe kudaden kasar wurin biyan basuka.

Alkaluman CBN din ya bayyana cewa kasar ta biya Dala miliyan 112 don biyan bashi a watan Janairun 2023.

Najeriya ta kuma biya Dala miliyan 288 a watan Faburairu yayin da ta biya Dala miliyan 400 a watan Maris.

Nawa ne Jimillar basukan da Najeriya ta biya?

Har ila yau, kasar ta biya Dala biliyan 92 a watan Afrilu na shekarar 2023 da kuma Dala miliyan 221 a watan Mayu.

Watan da yafi ko wane muni shi ne na watan Yuni wanda ya kai Dala miliyan 543 wanda ya fi ko wane wata yawa.

Rahoton kamar yadda CBN ya tabbatar, wadanda ake biya bashin sun hada da kasar Sin da Faransa.

Sauran sun hada da Japan da Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka da kuma Bankin Raya Musulunci.

Kara karanta wannan

Ministan Abuja: Tsohon Gwamnan PDP Ya Fayyace Gaskiyar Wanda Yake Wa Aiki Tsakanin Tinubu da APC

Tinubu Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Cin Bashi A Najeriya

A wani labarin, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin kawo karshen dogaro da basuka da kasar ke yi don gudanar da ayyukan ci gaban kasa.

Tinubu ya ce ba zai lamunci irin wannan lamari ba duba da yadda kasar ke samun kankanin kudin shiga.

Wannan na zuwa ne bayan kasar ta biya bashin da ya kai Dala biliyan daya ga kasashen Sin da Faransa da Bankin Duniya da kuma Bankin Raya Afirka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.