Bikin Murna Ya Barke a Gabon Yayin da Sojoji Suka Karbe Mulki Daga Shugaban Kasa Ali Bongo, Hotuna Sun Bayyana
- Jami'an sojoji a Gabon sun bayyana a talbijin din kasar a ranar Laraba don ayyana cewa sun karbe mulkin kasar
- Wannan al'amari ya haifar da bikin murna sannan mutane sun fito titunan babban birnin kasar don nuna farin ciki
- Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban kasa Ali Bongo Ondimba ya lashe zaben kasar, wanda hakan ya ba iyalinsa damar ci gaba da mulkin kasar
Libreville, Gabon - Masu goyon bayan kwace mulki da sojoji suka yi a kasar Gabon da dama sun yi tururuwar fitowa kan titinunan unguwanninsu.
Hotunan da Legit.ng ta gano sun nuna al'ummar garo suna jinjinawa dakarun rundunar tsaro a yankin Plein Ciel da ke Libreville, babban birnin kasar Gabon.
Rundunar sojojin kasar Gabon ta sanar da hambarar da gwamnatin shugaban kasa Ali Bongo.
Juyin mulkin Gabon: Yan farar hula na murna
Al Jazeera ta watso shirin kai tsaye kan halin da ake ciki a Libreville kan rikicin Gabon a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Iyalan Bongo ne ke mulkin kasar da ke yammacin Afirka tun bayan samun yancin kai daga kasar Faransa a shekarar 1960.
Wannan juyin mulkin babban koma-baya ne ga Najeriya, Shugaban kasa Bola Tinubu, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), da kawayenta da ke fafutukar ganin sun karbe mulki daga hannun masu mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.
Sojoji Sun Kifar Da Gwamnatin Shugaba Ali Bongo Na Kasar Gabon
Da farko mun ji cewa sojoji sun bayar da sanarwa na kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo a kasar Gabon, bayan ya lashe zaben da ya gudanara a kasar a ranar Asabar, 26 ga watan Agusta.
Bongo, wanda ya hau karagar mulki bayan mutuwar mahaifinsa a shekarar 2009, ya lashe zabe a karo na uku.
Sojojin Nijar sun datse samar da wuta da ruwa zuwa ofishin jakadancin Faransa
A wani labari na daban, mun ji cewa sojojin juyin mulki a Nijar sun bayar da umurnin datse hamyar samar da wuta da ruwa zuwa ofishin jakadancin kasar Faransa da ke kasar.
Sojojin sun kuma bayar da umurnin dakatar da kai abinci zuwa ofishin jakadancin da ke Zinder.
Asali: Legit.ng