Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur, Ministan Yaɗa Labarai
- Ministan Yaɗa Labarai na Tarayya, Mohammed Malagi, ya bayyana amfanin cire tallafin fetur ga rayuwar yan Najeriya
- Bayan gana wa da gwamnan Neja, Malagi ya ce mutane zasu sha walaha a karon farko amma daɗin na nan zuwa a gaba
- Ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta tara makudan kuɗaɗe kuma ta tura wa jihohi domin tallafawa jama'a
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Malagi, ya ce nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara ganin amfanin cire tallafin man fetur a ƙasa.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da ya karbi bakuncin Gwamna Umar Bago na jihar Neja a ofishinsa da ke birnin tarayya Abuja, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Mista Malagi ya ce Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki matakin dakatar da biyan kuɗin tallafin man fetur ne domin amfanin kasa.
Ministan ya ci gaba da cewa, tun daga lokacin da aka cire tallafin zuwa yanzu, gwamnatin tarayya ta tara makudan kudaden tallafin da aka cire.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me gwamnatin Tinubu ta yi da kuɗin?
A cewar Ministan, gwamnatin tarayya ta tara kuɗi masu yawa bayan cire tallafi, wanda a halin yanzun an raba wa jihohi domin daƙile raɗaɗin cire tallafin fetur ga talakawa.
A kalamansa ya ce:
“Za ku yarda da ni cewa tallafin man fetur da aka cire a zahiri yana da amfani ga ‘yan Najeriya. Mun sha maimaita cewa za a ji zafin wannan cirewar na ɗan lokaci kafin daɗin ya zo, za a ga amfaninsa."
“A cikin ɗan kankanin lokaci an tara maƙudan kuɗade kuma an tura wani bangare na kudaden zuwa jihohi ta yadda zasu daƙile raɗaɗi da wahalhalun da mutane suka shiga bayan cire tallafin."
Ikon Allah: Gwamnan Arewa Ya Lale Kudi Sama da Biliyan Ɗaya Ya Siyo Motoci 10 Domin Taimaka Wa Talakawa
Ministan ya kuma bayyana kwarin guiwar cewa gwamnatin Tinubu zata bada fifiko wajen aiwatar da ajandarsa guda takwas domin amfanin ‘yan Najeriya, Guardian ta tattaro.
Jam'iyyar APC Ta Kara Haddasa Ruɗani a PDP
A wani rahoton na daban an shiga ruɗani yayin da sunan Wike ya shiga jerin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC a jihar Bayelsa.
Tun a farkon watan nan, PDP ta kaddamar da kwamitin kamfe kuma tsohon gwamnan Ribas ɗin yana ciki a matsayin mamba.
Asali: Legit.ng