Prince Oyebola: An Zabi Dan Shekara 53 a Matsayin Sabon Sarki a Jihar Oyo

Prince Oyebola: An Zabi Dan Shekara 53 a Matsayin Sabon Sarki a Jihar Oyo

  • Masu naɗa sarki a Masarautar Iseyin sun zaɓi Prince Olawale Oyebola a matsayin sabon Sarki ranar Talata, 29 ga watan Agusta, 2023
  • Rahoto ya nuna kafin fara kaɗa kuri'a a Masarautar, sai da jami'an tsaro suka kewaye wurin domin tabbatar da doka da oda
  • Sabon Sarkin da aka zaɓa tare da iyalansa suna zaune ne a ƙasar Amurka kuma a can yake aiki amma yana tallafawa mutanen yankinsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Oyo state - Yarima Olawale Oyebola ya samu nasarar zama sabon Sarkin Iseyin wanda ake kira da Aseyin na Iseyin a jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Majalisar Sarakunan da ke da alhakin naɗa Sarki sun bayyana sunan Oyebola ne biyo bayan zaben da suka gudanar a fadar Aseyin ranar Talata, 29 ga watan Agusta, 2023.

Aseyin na Iseyin a jihar Oyo.
Prince Oyebola: An Zabi Dan Shekara 53 a Matsayin Sabon Sarki a Jihar Oyo Hoto: thenation
Asali: UGC

Mambobin majalisar naɗa Sarkin sun isa fadar masarautar da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Talata bayan jami'an tsaro sun kewaye Masarautar domin tabbatar da doka da oda.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Daba Da Haɗin Kan 'Yan Sanda Sun Kai Kazamin Hari Sakatariyar Jam'iyya, Sun Yi Ɓarna

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an fara kaɗa kuri'ar zaɓen Sarkin kamar yadda jami'an gwamnatin ƙaramar hukumar Iseyin da jami'an tsaro suka tsara, komai ya tafi babu tangarɗa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakamakon kuri'un da aka kaɗa sun nuna cewa Yarima Olawale Oyebola ne a kan gaba kuma shi ya samu nasara.

Sabon Sarkin zai zama Aseyin na 30 a tarihin masarautar

A halin yanzu, Prince Oyebola zai zama shi ne Aseyin na 30 a tarihin masarautar Iseyin bayan rasuwar marigayi Dakta Abdganiy Salawudeen Adekunle Oloogunebi Ajinese na 1.

Jaridar Tribune Online ta tattaro cewa sabon Basaraken yana zaune a ƙasar Amurka tare da iyalansa kuma a can yake aiki.

Haka zalika a ko da yaushe yana fifita walwala da jin daɗin al’umma, wanda hakan ya sanya ya kafa gidauniyarsa ta ilimi.

Kara karanta wannan

Za a yi ta: Faransa ta daga yatsa ga sojin Nijar bayan umarnin korar jakadanta a kasar

A karkashin wannan gudauniya ne, ɗaliban da ke karatu a manyan makarantun gaba da Sakandire 'yan asalin yankinsa su ke samun tallafin karatu.

Sanata Barau Ya Gwangwaje Dalibai Sama da 600 da Tallafin Karatu a Kano

A wani rahoton kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin ya bai wa ɗaliban jami'ar BUK 628 tallafin karatu.

Daliban, waɗanda aka zaƙulo daga mazabar Kano ta Arewa, mataimakin shugaban majalisar dattawan yan ba kowane ɗaya Naira 50,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262