Fasto David Oyedepo Ya Bayyana Yadda Ya Ke Sauya Jiragen Sama Kamar Keken Hawa A Cocinsa
- Faston cocin Living Faith Worldwide, David Oyedepo ya bayyana yadda ubangiji ya albarkaci cocinsa da jiragen sama masu tarin yawa
- Oyedepo ya bayyana haka ne a cikin wata huduba da ya yi inda ya ce a cocinsa su na sauya jiragen sama kamar kekunan hawa
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Fasto Oyedepo shi ne yafi kowa kudi a cikin Fasocin Najeriya da kimanin kudi har Dala miliyan 150
Jihar Ogun – Shahararren Fasto David Oyedepo ya bayyana yadda ya ke sauya jiragen sama a cocinsa kamar keken hawa.
Oyedepo wanda shi ne shugaban cocin Living Faith Worldwide ya ce wannan na daga cikin albarkan da ubangiji ya yi musu a cocin.
A ina Oyedepo ya bayyana haka?
Oyedepo a cikin wata huduba ya ce lokacin da ubangiji ya sanar da shi zai mallaki jirgi da shi da mambobin cocinsa ba su yarda ba, The Discoverer Nigeria ta tattaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa:
“Ubangiji ya fada mana zamu samu jirgi, idan da a tsarin mu ne sai mun kai shekaru 10 kafin tsara siyan jirgin.
“A yanzu muna sauya jirgi kaman kamar wasu kekunan hawa saboda yadda ubangiji ya albarkaci rayuwarmu da kuma hana mu bakin ciki.”
Faston ya kara da cewa akwai wadanda ke addu’ar samun jirgin sama, amma ko da sun samu dole su siyar saboda irin lissafin da ke kan jirgin a wata, amma idan lokacin mallakar ya yi ba matsala, PM News ta tattaro.
Shin Oyedepo ya fi kowa kudi cikin Fastoci?
Ya ce:
“Ba mu yi addu’ar samun jirgin ba, mu yi meye da jirgi? An tambayen wane irin jirgi na ce ko wane saboda bansan sunan jirgi ko guda daya ba.”
Rahotanni sun bayyana cewa Fasto Oyedepo shi ne yafi kowa kudi a cikin Fasocin Najeriya da kimanin kudi har fiye da Dala miliyan 150.
“Budurwarsa Ta Ba Shi Kunya”: Malamin Addini Ya Yi Tsalle Daga Ginin Bene Mai Hawa 2, Ya Mutu a Anambra
Ya na da jirage har guda hudu wanda ya hada da jirgi kirar Gulfstream V wanda akalla kudinsa ya kai Dala miliyan 30.
Fasto Ayodele Ya Yi Martani Game Da Goyon Bayan Peter Obi
A wani labarin, shugaban cocin INRI, Fasto Elijah Ayodele ya bayyana dalilin da yasa Fasto David Oyedepo da Paul Enenche ke goyon bayan Peter Obi a zaben shugaban kasa.
Ayodele ya ce bai kamata 'yan Najeriya su zargi fastocin ba don sun nuna ra'ayinsu sai dai sun yi haka ne don neman sauyi wa kasar.
Asali: Legit.ng