Femi Falana Ya Bukaci a Koma Amfani Da Naira a Harkar Kasuwanci Tsakanin Najeriya Da China

Femi Falana Ya Bukaci a Koma Amfani Da Naira a Harkar Kasuwanci Tsakanin Najeriya Da China

  • Babban lauya Femi Falana ya bukaci a koma amfani da naira wajen kasuwanci tsakanin 'yan Najeriya da 'yan China
  • Ya ce har yanzu yarjejeniyar kasuwanci da aka ƙulla tsakanin ƙasashen biyu tana nan
  • Sai dai ya ce babban bankin Najeriya (CBN), baya bai wa 'yan ƙasa damar amfana da tsarin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Babban lauya kuma ɗan rajin kare haƙƙin bil'adama Femi Falana ya buƙaci 'yan kasuwa na Najeriya su riƙa kasuwanci da 'yan ƙasar Sin wato China da Naira ko kuma Yuan.

Femi Falana ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya fitar a ranar Litinin, 28 ga watan Agusta kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Falana ya bukaci 'yan Najeriya su fara kasuwanci da naira
Femi Falana ya buƙaci 'yan Najeriya su fara kasuwanci da naira a tsakaninsu da China. Hoto: Central Bank of Nigeria, Femi Falana
Asali: Facebook

Falana ya fadi dalilin bukatar kasuwanci da naira tsakanin Najeriya da China

Femi Falana ya bayyana cewa wannan wata yarjejeniya ce da aka ƙulla tun shekarar 2018 a tsakanin Najeriya da ƙasar Sin, wato a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana a Yanayin Da Ta Tarar Da Tattalin Arziƙin Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce yarjejeniyar wacce darajarta ta kai kuɗin ƙasar Sin RMB biliyan 16, daidai da naira biliyan 720, za ta taimaka wajen samar da isassun kuɗaɗen da 'yan ƙasashen biyu za su yi kasuwanci da su.

Ya ce amfani da tsarin zai taimaka wajen sauƙaƙa kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu saboda za a daina dogaro da dalar Amurka wajen gudanar da hada-hada.

CBN, IMF da bankin duniya suka ɓata shirin

Falana ya bayyana cewa Sai dai a cewar Hukumar Ba da Lamuni ta Duniya (IMF), Bankin Duniya da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) ne suka haɗu suka lalata shirin.

Falana ya ƙara da cewa dalilinsu na yin hakan shi ne domin barin dalar Amurka ta ci gaba da cin karanta babu babbaka a harkokin kuɗi na Najeriya.

Ya kuma ce a binciken da ya gudanar, ya gano cewa har yanzu yarjejeniya na nan, amma CBN ya ƙi ya bai wa 'yan Najeriya damar yin kasuwanci da naira ko Yuan na ƙasar Sin.

Kara karanta wannan

An Kuma Yin Juyin Mulki a Wata Kasar Afrika Ta Yamma Ta Daban? Bayanai Sun Fito

A rahoton The Nation, Falana ya buƙaci 'yan Najeriya da su fara amfani da naira wajen biyan kuɗaɗen kayayyakin da suka siya daga China.

'Yan kasuwa sun abinda za a yi mai ya sauko tashi ɗaya

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan jawabin da wani daga cikin 'yan kasuwar man fetur ta Najeriya (IPMAN) ya yi kan abinda za a yi farashin man fetur ya sauko tashi ɗaya.

Ya bayyana cewa da zarar Gwamnatin Tarayya ta gyara duka matatun man Najeriya za a samu sauƙi a kan kowace lita ɗaya ta man fetur kan yadda ake sayar da shi a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng