Alkawari ya cika: An soma hada-hadar kudaden kasar Sin na Yuan a Najeriya

Alkawari ya cika: An soma hada-hadar kudaden kasar Sin na Yuan a Najeriya

Labarin da muke samu na tabbatar mana ne da cewa babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) ya soma fara saye da sayerwar kudaden kasar Sin watau China na Yuan kamar yadda yakeyi da kudin kasar Amurka na Dala a baya.

Wannan dai na nufin yanzu wannan daddadar yarjejeniyar da kasar Najeriya ta shiga da takwarar ta ta kasar Sin din a lakacin baya sadda Shugaba Buhari ya kai wata ziyarar aiki ta soma aiki.

Alkawari ya cika: An soma hada-hadar kudaden kasar Sin na Yuan a Najeriya
Alkawari ya cika: An soma hada-hadar kudaden kasar Sin na Yuan a Najeriya

KU KARANTA: Yan ta'addan Boko Haram sun tafka ta'asa a wasu kauyuka a Borno

Legit.ng ta samu cewa masana tattalin arziki da hada-hadar kudade sun bayyana cewa ana sa ran wannan ya farfado da darajar kudin Najeriya na Naira.

A wani labarin kuma, Rundunar sojin saman Najeriya Nigerian Air Force (NAF) a ranar Alhamis din da ta gabata ta kara yaye matukan jiragen yaki a makarantar koyon tukin jiragen dake a garin Kainji.

Da yake jawabi a wajen yaye daliban, Hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar da shugaban makarantar Air Vice Marshal Mohammed Idris ya wakilta ya bayyana yaye daliban a matsayin babban cigaba a kasar musamman ma wajen yaki da take yi da 'yan ta'adda.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng