Ministocin Tinubu: Shehu Sani Ya Yi Wa Umahi Shagube Kan Rike Mukamai Biyu
- Ministan ayyuka, David Nweze Umahi, ya riƙe muƙamin sanatan Ebonyi ta Kudu a tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2023
- Daga nan sai shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba shi muƙamin minista a cikin sabuwar gwamnatinsa
- Sai dai, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi zargin cewa Umahi ya na riƙe da muƙamai biyu, sanata da minista
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya caccaki ministan ayyuka na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, David Nweze Umahi.
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wacce a baya aka sani da Twitter) a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, Shehu Sani ya yi zargin cewa Umahi ya haɗa ya riƙe kujerar minista da ta sanata.
Tsohon sanatan ya yi bayanin cewa tsohon gwamnan na jihar Ebonyi, ya riƙe muƙaman guda biyu da hannayensa na hagu da na dama.
A kalamansa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ɗan uwa Umahi yana riƙe da kujerar sanata da hannunsa na dama sannan yana riƙe da kujerar minista da hannunsa na hagu, ko da a ce za a samu sauyin yanayi."
Ƴan Najeriya sun yi martani kan shaguɓen da Shehu Sani ya yi wa Umahi
Ƴan Najeriya sun garzaya sashen yin sharhi inda suka bayyana mabambantan ra'ayoyi dangane da rubutun da Shehu Sani ya yi.
@ChukwunyeluOrji ya rubuta:
"Tsoron Peter Obi. Peter Obi na nan tafe."
@RashwalRashwal ya rubuta:
"Na rantse Shehu Sani ya fara shan wani abu...Ba ko da yaushe ya ke akan daidai ba."
@Doc_steena ya rubuta:
"Ka da ku ga laifinsa oh, dukkaninsu suna jiyo ƙamshin abin da ke tafe. Su cigaba da more ɗanɗanonsu kamar yadda ogansu zai ɗanɗana ne kawai."
Hadimin Atiku Ya Fadi Iya Wa'adin Da Ya Ragewa Bola Tinubu a Kan Kujerar Shugabanci, Ya Ba Shi Shawara
Engr_Stanley_EC ya rubuta:
"Ba ya son ya yi saki na dafa."
@theo_enakhe ya rubuta:
"Dubi irin wannan abun... Ta yaya sanata mai ci zai zama minista. Wai ba wata doka ne da ta haramta hakan?"
Shehu Sani Ya Yaba Da Shirin Hadewar PDP, LP
A wani labarin na daban kuma, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya ya yi maraba da shirin hadewar da jam'iyyun adawa su ke yi.
Shehu Sani ya bayyana batun dunƙulewar jam'iyyun adawan a matsayin abu mai kyau ga dimokuraɗiyyar ƙasar nan.
Asali: Legit.ng