Ba Za Ta Yi Wu Ba: Tinubu Ya Ce Dole a Bijirewa Turbar Da Buhari Ya Daura Najeriya
- Bola Ahmed Tinubu ba zai lamunta da yadda ake kashe duk abin da ya shigo aljihu a biyan bashi ba
- Gwamnatin baya ta karbo aron makudan kudi a gida da waje, hakan ya jawo ake fama da bashi
- Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta karar da arziki kasa a kan basoshin ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya nuna ba zai amince da tsarin da ake tafiya a kai na kashe kusan duka lalitar gwamnati wajen biyan bashi ba.
A ranar Lahadi, Daily Trust ta rahoto Shugaban Najeriyan ya na sukar yadda kudin-shiga su ke karewa duk a biyan bashin kudin da aka aro.
Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya bayyana haka da ya halarci bikin bude taron kungiyar lauyoyi na NBA da aka yi a filin wasan MKO Abiola.
Jawabin Shugaban kasa Bola Tinubu
"Za mu cigaba da kashe 90% na kudin shiganmu wajen biyan bashin kudi a kasashen waje? Hanyar hallaka ce. Ba za ta yiwu a cigaba ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tilas mu kawo sauyin da su ka zama dole ga kasarmu, sai mun farka daga gyangyadin da mu ke yi sai girmama mu a kasashen duniya."
- Bola Tinubu
Shugaban kasar ya gabatar da jawabi mai ban sha’awa a gaban lauyoyi 16, 190 da ke halartar gagarumin taron da aka saba yi a duk shekara.
A wajen ne shugaban kasar ya shaida cewa da farko za a koka da manufofin da ya fito da su, amma ya tabbatar da za a ga amfaninsu nan gaba.
Punch ta rahoto Bola Tinubu ya na mai cewa saboda yaran da za a haifa nan gaba ya fito da tsare-tsaren da wasu su ke kokawa da su a Najeriya.
"Dole mu yi abin da za mu yi domin kai kasar nan ta cin ma burinta. Ba batun ni ko ku ake yi ba, ana maganar al’umma masu zuwa ne nan gaba."
- Bola Tinubu
A cewarsa, Gwamnatinsa za ta kawo irin sauyin da aka gani a bangaren shari’a a lokacin da ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas a Legas.
Tony Elumelu ya yabi manufofin Tinubu wanda ya gaji bashin kudi masu yawa daga hannun gwamnatin Muhammadu Buhari a karshen Mayu.
Tinubu bai son filaye a Abuja
Rahoton da mu ka samu a baya shi ne Shugaban Najeriya ya nuna bai bukatar a raba masa filaye a Abuja, sai dai ayi wa al’umma aikin da za a mora.
Mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ministansa watau Nyesom Wike ya gaggauta kammala aikin titin jirgin kasan birnin Abuja.
Asali: Legit.ng