Tinubu Ya Fadawa Wike Abin da Yake So a Abuja - Idan Na Nemi Fili Ka da a Yanka Mani
- Bola Ahmed Tinubu bai bukatar ya nemi kyautar fili daga wajen babban ministan birnin tarayya
- Shugaban kasar Najeriyan ya fadawa Nyesom Wike cewa ba zai nemi a yanka masa fuloti a Abuja ba
- Abin da Shugaba Bola Tinubu yake so ministan ya yi shi ne ya kammala aikin jirgin kasan birnin
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya karasa aikin jirgin kasan garin Abuja.
Legit.ng Hausa ta lura Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya samu halatar taron kungiyar lauyoyi na kasa watau NBA wanda aka kaddamar a jiya.
Da ya ke magana wajen bude taron, The Cable ta ce shugaban kasa ya ce zai so a kammala aikin dogon Abuja, domin al’umma su amfana.
Tinubu: Jirgin kasan Abuja ya na da amfani
Bola Tinubu ya ce shi kan shi zai so ya shiga jirgin, saboda haka ya bukaci sabon ministan ya yi bakin kokarinsa domin ganin an kammala.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A rahoton da aka samu daga Nairaland, an ji yadda shugaban Najeriyan ya jaddadawa tsohon gwamnan na Ribas muhimmancin dogon.
"Ina iya ganin babbanmai masaukin bakinmu, uban gidan Abuja. Ka dage da haka, ina so in shiga jirgin kasan ka a tuka ni.
Idan na tambaye ka kyautar fili, ka da ka ba ni, amma ka samar da jirgin kasan cikin birni domin dinbin al’ummar Najeriya."
- Bola Tinubu
Wike zai biya mazauna Abuja hakkokinsu
Tuni har ministan ya tsaida wa’adi domin a biya mutane hakkokinsu domin su bar gidajensu da ke wuraren da titin jirgin zai bi.
Wike ya bayyana haka a ranar Laraba da ya ziyarci tashar jirgin kasa da ke Idu da filin jirgin sama domin ya ganewa idanunsa.
Ministan ya zauna da Festus Keyamo domin ganin yadda za a sallami mazauna da gidajensu su ka fado ta yankin da titin jirgin zai bi.
Nyesom Wike ya zo da shirin aiki
Nyesom Wike ya shiga ofis a makon da ya gabata, ya kama shirin aiki babu kama hannun yaro, ya ce zai dawo da darajar Abuja.
Tun a lokacin aka aji sabon ministan tarayyar ya fadawa ma’aikatan da ba su da niyyar aiki a birnin Abuja su canza ma’aikata.
Asali: Legit.ng