Sojin Saman Najeriya Sun Bankado Matatun Man da Ake Tace Mai Ba Bisa Ka’ida Ba, Sun Kone Su Kurmus
- Rahotanni sun bayyana yadda sojojin saman Najeriya suka samu nasarar fatattakar ‘yan ta’adda a bangarori daban-daban na kasar nan
- An kuma kone wurin da ake aikin tace danyen man fetur ba bisa ka’ida ba, inda aka kone wani jirgin ruwa na Cotonou
- A Arewa kuwa, an fatattaki ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas mai fama da yawaitar ‘yan tada kayar baya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta lalata wasu haramtattun wuraren tace danyen mai da jiragen ruwa a jihar Rivers, TheCable ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar NAF, Edward Gabkwet ya fitar, ya ce an kai hare-haren ne a ranar Lahadi a wuraren da ke Cawthorne Channels, Bille da Gogokori a karamar hukumar Degema ta Rivers.
Ya ce wani jirgin ruwan Cotonou da aka lura yana lodin albarkatun mai da aka tace ba bisa ka'ida ba, kuma ya nufi cikin ruwa, shi ma aka hade tare da lalata shi a Gogokori.
Ya ce an kuma kai irin wannan hari a wasu wurare biyu a Idama na karamar hukumar Akuku-Toru da Omoma a karamar hukumar Degema ta jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gabkwet ya ce bisa ga dukkan alamu ana aikin tace man fetur ba bisa ka'ida ba a wuraren da ke da tafkunan da ake zargin suna dauke da kayan aikin tacewa.
Wasu wuraren da aka farmaka a jihar Cross River
Kakakin ya ce, a ranar 25 ga watan Agusta, an kuma lalata sansanonin ‘yan bindiga da na ‘yan fashi da sunan sansanin Big Joe, sansanin Sunny, sansanin Davids duk a karamar hukumar Bakassi da kuma sansanin Amos da ke Calabar a kudancin karamar hukumar Cross River.
Ya kara da cewa an ba da izinin kai hare-haren ta sama ne bayan da aka tabbatar da wuraren da aka farmakar ana wadannan miyagun da ayyukan..
Ya kara da cewa:
"Wadanda suka yi yunkurin tserewa ta hanyoyin tserewa daban-daban su ma an farmake su.
A yankin Arewa maso Gabas, Gabkwet ya ce an lalata maboyar ‘yan ta’adda a tsaunin Mandara, inda ya kara da cewa an kashe ‘yan bindiga da dama a aikin.
An hallaka 'yan ta'adda a Borno
Kungiyar Jama'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wal-Jihad (JAS) ta Boko Haram, ta kara shan kashi a hannun dakarun sojin saman Najeriya a jihar Borno.
Jiragen yakin dakarun sojin saman sun yi luguden wuta a maboyar ƴan ta'addan da ke a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Harin an kaddamar da shi ne ta hanyar amfani da jiragen Super Tukano a sansanin Ali Ngulde a yankin Arewa maso Gabas na tsaunin Mandara a ranar 6 ga watan Yunin 2023.
Asali: Legit.ng