“Na Tuba Daga Yanzu”: Budurwa Ta Kona Dukka Kayanta Da Ke Nuna Tsaraici, Ta Zama Kirista Ta Gaske
- Wata matashiya ta tattara gaba daya kayanta masu nuna tsaraici sannan ta cinna masu wuta bayan ta yanke shawarar zama kirista ta gaske
- Matashiyar, Precious Thamani, ta wallafa wani bidiyo da ke nuna lokacin da ta kona kayan sannan ta ce yanzu ita Kirista ce
- Precious ta shahara a TikTok saboda sadaukarwar da ta yi, yayin da mutane da dama suka goyi bayan abun da ta yi
Wata matashiyar budurwa ta saki bidiyo da ke nuna lokacin da ta kona gaba daya kaya masu nuna tsaraici da ta mallaka.
A bidiyon da aka wallafa a ranar Asabar, 27 ga watan Agusta, Precious Thamani ta ce ta yanke shawarar zama kirista ta gaske.
Precious ta ce ta dade tana sakaci da rayuwarta na kirista sannan cewa a yanzu ta shirya daukar abun da zafi.
Mai Da Tsohuwa Yarinya: Yadda Mai Kwalliya Ta Sauya Fuskar Yar Shekaru 81 Ta Zama Tamkar Matashiya, Bidiyon Ya Yadu
Ta fito da kayayyakin da ke kwanciya a fatar jikinta idan ta sanya su sannan ta cinna masu wuta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Budurwa ta zama Kiristan gaske, ta kona dukka kayanta masu nuna tsaraici
Precious ta ce tana alfahari da matakin da ta dauka sannan ta ayyana cewa a yanzu ta zama baiwar Allah ta gaskiya.
Daya daga cikin hotunan da aka gani a wallafarta ya nuna yadda take shiga a baya kafin ta yanke shawarar tuba.
Ta rubuta a bidiyon:
"Gaskiya ina ta shakkar wallafa wannan, amma babu abin jin kunya a ciki. Ina alfahari da zama baiwar Allah."
Mutane da dama a TikTok sun goyi bayan abun da Precious ta yi, sannan suka garzaya sashin sharhi don jinjina mata.
Kalli bidiyon a kasa:
Martanin yan TikTok yayin da budurwa ta kona kayanta masu nuna tsaraici
@BeautifulSoul ta ce:
"Zan so ganin yadda kike shiga a yanzu. Ina alfahari da ke, godiya gare ki da kika amsa kiran Allah."
@Mitchie-dhee ta ce:
"Ubangijinmu ya sake yinsa. Muna farin ciki."
@moitoi ta yi martani:
"Ina ta fadi cewa ina fafutuka da shiga ta kamala a matsayina na matashiyar Kirista. Ina so wa kaina wannan."
Ango ya saka siket zuwa wajen daurin aurensa
A wani labari na daban, mun ji cewa wani matashi dan Najeriya ya yi abun da ba a saba gani ba yayin da ya angonce da amaryarsa Baturiya.
Sabanin yadda aka saba gani, angon ya saka siket da kwat zuwa wurin daurin auren nasu yayin da yake cike da farin ciki.
Asali: Legit.ng